• English
  • Business News
Saturday, August 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City

by Sulaiman and Rabilu Sanusi Bena
2 months ago
in Wasanni
0
De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kevin de Bruyne ya kammala komawa Napoli bayan da dan wasan tsakiyar Belgium din ya bar Manchester City inda ya buga wasanni 422 ya kuma zura kwallaye 108 a karshen kakar wasar bana. De Bruyne zai hadu da tsohon kocin Chelsea da Tottenham Antonio Conte, wanda shi ne kocin zakarun na kasar Italiya a halin yanzu.

Napoli ta sanar da sanya hannun dan wasan mai shekaru 33 a shafukanta na sada zumunta inda ta yi wani rubutu a sama dake nuna ” Sarki Kev” ya zo, Kevin ya bar Manchester City bayan ya shafe shekaru 10 a kulob din, inda ya lashe manyan kofuna 19 bayan da ya zo daga Wolfsburg a shekara ta 2015.

  • An Bude Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka A Changsha
  • Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

De Bruyne ya taimaka wa City ta lashe kofunan Firimiya shida, Kofin League biyar da Kofin FA guda biyu, sai kofin gasar zakarun Turai na farko da kungiyar ta taba lashewa a shekarar 2023, sai kuma kofunan Firimiya uku a jere yayin da kungiyar Pep Guardiola ta zama kungiya ta biyu daga kasar Ingila da ta taba samun wannan nasarar.

Labarai Masu Nasaba

Osimhen Ya Kammala Komawa Galatasaray

Kare Ya Ciji Tsohon ÆŠan Wasan Barcelona A Mazakuta

An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki yan wasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan da Rayan Cherki daga Lyon.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

Next Post

Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

Related

Osimhen Ya Kammala Komawa Galatasaray
Wasanni

Osimhen Ya Kammala Komawa Galatasaray

1 day ago
Kare Ya Ciji Tsohon ÆŠan Wasan Barcelona A Mazakuta
Wasanni

Kare Ya Ciji Tsohon ÆŠan Wasan Barcelona A Mazakuta

2 days ago
Salisu Yusuf Ya Ajiye Aikinsa Na Kocin Nasarawa United
Wasanni

Salisu Yusuf Ya Ajiye Aikinsa Na Kocin Nasarawa United

3 days ago
Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON
Wasanni

Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON

4 days ago
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje
Da É—umi-É—uminsa

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

5 days ago
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
Wasanni

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

6 days ago
Next Post
Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

LABARAI MASU NASABA

Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin FaÉ—aÉ—a Ayyukanta

Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin FaÉ—aÉ—a Ayyukanta

August 2, 2025
Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir

Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir

August 2, 2025
Kwamitin Tantance Makarantun Gaba da Sakandire Na Bogi Ya Yi Wa Yankin Funtua Dirar Mikiya

Kwamitin Tantance Makarantun Gaba da Sakandire Na Bogi Ya Yi Wa Yankin Funtua Dirar Mikiya

August 2, 2025
Yarjejeniyar Dala Biliyan Ɗaya Da Ƙasar Brazil Za Ta Haɓaka Fannin Noma A Nijeriya —Tinubu

Yarjejeniyar Dala Biliyan Ɗaya Da Ƙasar Brazil Za Ta Haɓaka Fannin Noma A Nijeriya —Tinubu

August 2, 2025
ADC Za Ta Kayar Da Tinubu A 2027 – Dino Melaye

ADC Za Ta Kayar Da Tinubu A 2027 – Dino Melaye

August 2, 2025
Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

August 2, 2025
Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi HaÉ—in Gwiwa

Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi HaÉ—in Gwiwa

August 1, 2025
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

August 1, 2025
2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa

2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa

August 1, 2025
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

August 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.