Ɗan wasan tsakiyar Belgium, Kevin De Bruyne, ya bayyana cewa zai bar Manchester City a ƙarshen wannan kakar wasa, bayan shafe shekaru 10 yana taka leda a ƙungiyar.
Ɗan wasan mai shekaru 33, ya ce kwantiraginsa zai ƙare a bana, kuma lokaci ya yi da zai bar Etihad Stadium.
- Tinubu Da Kwankwaso Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Dokta Idris Dutsen Tanshi
- Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata
Tun daga shekarar 2015 da ya koma ƙungiyar daga Wolfsburg, De Bruyne ya lashe kofuna 16 da suka haɗa da gasar Firimiyar Ingila sau shida da kuma kofin Zakarun Turai a 2023.
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce De Bruyne “yana daga cikin mafiya ƙwarewa a matsayin ɗan wasa a tsakiya da duniya ta taɓa gani.”
De Bruyne ya buga wasanni 413 tare da zura ƙwallaye 106 a City.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce: “Ko muna so ko ba mu so, lokaci ya yi da za mu yi bankwana.”
Ƙungiyar Manchester City ta ce za ta shirya wani bikin bankwana na musamman domin girmama ɗan wasan kafin kakar ta ƙare.
De Bruyne ya koma City daga Wolfsburg a kan fan miliyan 55, kuma ya taimaka sosai wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu, ciki har da lashe kofin Zakarun Turai karo na farko a tarihinta, inda suka doke Inter Milan a wasan ƙarshe a birnin Istanbul.
Sai dai ɗan wasan ya sha fama da rauni a ‘yan shekarun nan, inda ya shafe watanni biyar yana jinya a kakar da ta wuce.
A kakar bana, ya buga wasanni 26 kacal a dukkanin gasa.
De Bruyne, ya fara wasan ƙwallon kafa a kulob din Genk na Belgium, kafin Chelsea ta saye shi a watan Janairu 2012 a kan fan miliyan bakwai.
Ya buga wa Chelsea wasanni tara kacal sannan aka tura shi aro zuwa Werder Bremen, daga nan ya koma Wolfsburg a 2013, kafin komawarsa City.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp