Jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da bayani kan yanayin demokuradiyyar Amurka a shekarar 2022, wanda ya bayyana hakikanin halin da kasar Amurka ke ciki a fannin demokuradiyya, da hakan ya fayyace matsalolin da Amurka ke fuskanta a wannan fanni, da rudani, da rikici, da ma kabalulolin da Amurka ta haifar wa duniya, ta hakan za a kara fahimtar ainihin alkiblar demokuradiyya iri na Amurka.
Daga shekarar 2001 zuwa yanzu, mutane a kalla dubu 900 sun mutu sakamakon yake-yake da matakan soja da Amurka ta dauka bisa hujjar yaki da ta’addanci, daga cikinsu dubu 335 fararen hula ne. Bayan ga haka, miliyoyin mutane sun ji raunuka, har ma fiye da miliyoyin mutane suka rasa gidajensu. A sa’i daya kuma, domin kare muradunta, Amurka ta yi amfani da takunkumi na kashin kai wajen cutar da wasu kasashe, har ma ta rufe ainihin muradunta na tada yake-yake da babakere ta hanyar yada demokuradiyya irin nata.
A yayin da aka cika shekaru 20 da kaddamar da yakin Iraki, dole ne wasu ‘yan siyasa na Amurka sun sake tunani don dakatar da tada zaune tsaye a sauran wurare bisa hujjar demokuradiyya, idan ba haka ba, wasu kasashe za su tabka hasara kamar Iraki. (Amina Xu)