Shalkwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ƙaryata rahoton da ke cewa an yi yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wani shafin yanar gizo ya wallafa cewa an kama wani Birgediya Janar da wasu jami’an soji da Hukumar Leƙen Asiri ta Soja (DIA) saboda zargin shirin juyin mulki.
- ‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe
- Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Rahoton ya kuma danganta soke bikin zagayowar ranar ’yancin kai na Njeriya na shekara 65 kan wannan zargin.
Da yake mayar da martani, Daraktan Bayanan Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce rahoton ƙarya ne, kuma an ƙirƙire shi ne domin tayar da hankalin jama’a.
Ya bayyana cewa an soke bikin ne saboda Shugaba Tinubu zai halarci wani muhimmin taro a ƙasashen waje, sannan dakarun sojoji sun mayar da hankali wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi da makami.
Gusau, ya ƙara da cewa binciken da ake yi kan wasu jami’ai 16 ba shi da alaƙa da wani juyin mulki, illa kawai don tabbatar da ƙwarewar aikin soja.
Ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa dakarun soji suna nan daram da goyon bayan kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da wannan rahoton.