Tun daga lokacin da aka maido da huldar diflomasiyya tsakanin Saudi Arabia da Iran, da sulhunta bangarori daban-daban na Falasdinu zuwa fadada tsarin kawancen ziri daya da hanya daya na BRICS mai ma’anar tarihi da kuma goyon baya ga shigar da kungiyar hadin kan afirka cikin kungiyar kasashe masu samun ci gaban tattalin arziki ta G20, huldar diflomasiyyar manyan kasashe mai salon dabi’un kasar Sin ke ci gaba da kawo kwanciyar hankali da hadin gwiwa a tsakanin kasashen da ba su ga-maciji da juna a baya.
Alkaluman bayanan binciken ra’ayoyin jama’a da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar a duniya shekaru biyu da suka gabata sun nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyi daga sassan duniya sun yaba kwarai da diflomasiyyar manyan kasashe da ke da dabi’u na kasar Sin. Sun yi amannar cewa, kasar Sin ta yi rawar gani wajen karfafa adalci da hangen nesa a tsakanin kasashen duniya.
- Dokokin Gyaran Haraji Sun Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
- Gwamnan Gombe Ya Aza Tubalin Gina Majalisar Dokoki Da Babbar Kotun Jiha Na Zamani
A cikin binciken, kaso 82.5 cikin dari na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun ce hikimar da kasar Sin ta yi wajen bullo da manufar “al’umma mai makomar bai-daya domin bil’adama” ta sanya kuzari mai dorewa ga kokarin gina kyakkyawar makoma ga dan Adam.
Haka nan kaso 84.5 cikin dari na masu bayyana ra’ayin sun aminta da shirin bunkasa ci gaban duniya, inda suka yi ammanar cewa samar da ci gaba ita ce hanyar warware matsalolin duniya da samun farin ciki ga dan Adam. Yayin da kaso 85.6 na mutanen suka ce tsaro wani ginshiki ne na samun ci gaba kuma ya kamata kasashe su yi aiki kafada-da-kafada wajen gina tsarin tsaro mai adalci da inganci da zai dore. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)