Duk da irin ribar da ake samu a fannin noman gwanda a Nijeriya, sai dai akasarin ‘yan kasar, sun yi watsi da damar da ake samo a fannin noman gwanda, sai dai, masana a fannin na ganin hakan na faruwa ne saboda rashin wayar masu da kai dangane da alfanun da ke tattare da noman gwanda, musamman ganin cewa, fannin bai bukatar sai ka tandi kudade masu yawa kafin ka shiga cikinsa ba.
Yadda Za Ka Yi Renon Irin Gwanda:
Babbar hanyar kuma mataki na farko a noman gwanda shi ne, ka fara renin irin da za ka Shuka gwandar.
Ka Tabbatar Ka Sayo Ingantaccen Irin Da Za Ka Shuka:
Ka samu wajen da ya fi dace wa, kayi gyaran wajen tare da kone sharar da ke wajen sai ka shuka irin mita biyar tsakanin kowanne iri haka, yana kai wa kimanin satuttuka kafin ya fara nuna ko kuma wuce haka.
Bayan wata biyu da shuka sai a nome ciyawar da ke gurin ka da a kima zubar da ciyawar a barta ta rube a gurin yadda za ta zama takin gargajiya.
Bayan wata daya zuwa biyu, sai ka canza wa mata waje, inda kake ganin zai fi gibin sama da mita biyar, inda kuma bayan watanni uku, sai ka sayo maganin feshi kayi wa kasar feahe, inda hakan zai sa ta yi saurin girma.
Har ila yau, bayan wata shida sai ka kara yin feshi, inda a cikin sati uku masu zuwa za ta kara yin kwau same, haka ka bar ta zuwa wata uku ko fiye da haka don ta kara yin karfi.
Kasar Noman Da Ta Fi Dace Wa :
Ka tabbatar da ka yi shukar a kasar noman da ya fi dace wa, musammn domin ka samu amfanin mai yawa, haka ana son ka yi shukar a kasar noman da ke lema.
Matakan Shuka Gwanda:
A wannan matakin, ana bukatar ka ciro ta daga wadanda suka fara fitowa daga cikin abin Da ka shuka Irin tun farko sai ka gina rami sai ka shuka ta.
Lokacin Da Ya Fi Dace Wa A Shukata:
Babu takamaiman lokacin da aka kebe na shukata, donin ako wanne lokaci na kakar noma za a iya yin nomanta har Ila yau kuma ta na jure wa ko wanne irin yanayi.
Kwana Nawa Take Yi Kafin Ta Fara Yin ‘Ya’ya ?
Ya danganta da ingantaccen Irin da aka shuka da kuma yadda nau’in Gwandar yake wasu, na kai wa tsawon shekaru hudu kafin su girma tun dg lokcin da aka shuka Irin, haka wasu na kai wa tsawon shekaru takwas kafin su girma.
Lokacin Dibanta:
Yayin da jikinta ya fara canza wa zuwa ruwan dorawa sai dai, wasu nau’in gwandar, ba sa canza wa zuwa ruwan dorawar idan sun nuna suna kuma kai wa watanni tara bayan an canza wa irin matsuguni daga inda raine shi.
Bishiya daya ta Gwanda, za a iya samar da kimanin Gwanda daga 75 zuwa 100 a shekara haka, ta na iya kai wa tsawon shekaru dari ana cire ‘ya’yanta, amma amfi fara samun amfanin ta daga shekaru uku zuwa shekaru hudu
Kasuwancin Gwandar:
A yayin da kake jiran ta kammala kai wa a girman ta, sai ka fara tuntubar masu bukatar saye ko kuma kasuwar da za ka kai fa don sayar wa, haka za ka iya tuntubar kamfanoni, musamman Wadanda ke sarrfa ta zuwa wasu nau’uakn yin kayan shafawa ko kayan lemon Kwalba ko sarrafa ta ta magunguna da sauransu.