Bai kamata Nijeriya ta kasance tana fama da talauci ba, bayan tana zaune a kan dimbin ma’adanai shinfide a sassan kasar nan.
Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake ya bayyana haka a taron baye kolin ma’adanai da kuma bayar da takardar shaida ga daliban da suka horo a kan sarrfa ma’adanai da kamfanin MinDiber ta dauki nauyi gabatarwa wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis da ta gabata.
- Gwamnatin Kwara Ta Tasa Keyar Mabarata 158 Zuwa Jihohinsu Na Asali
- Matsalolin Tsaro Da Ambaliya: ‘Yan Nijeriya Sun Sayo Abinci Daga Waje Na Tiriliyan 3 – CBN
Dakta Alake ya kuma ce, kawo shirin kera sarkar gwalagwalai tamkar kawo arziki cikin gida Nijeriya ne.
Ministan ya kuma bayar da kayan fara aiki ga wadanda suka koyi yadda ake kera gwalagwalan, ya ce mu su yanzu da aka basu kayan aiki tamkar an samar musu da hanyar cin abinci ne domin bunkasa rayuwarsu, ya kuma bukaci su bayar da nasu gudummawr domin bunkasa sashin hakar ma’adanai domin samun nasarar kasa gaba daya.
Ya kuma ce, “Babu wata jiha a kasar nan da ba ta da wani nau’in ma’adani da Allah ya shinfida a jihar, “a kan haka ban ga dalilimu na fama da talauci ba” in ji shi.
“Indan da mun yi abin da ya kamata a shekarun baya, inda mun mayar da hankalinmu zuwa bangaren ma’adanai, da bangaren ya isa ya rike mana tattalin arziki. Amma sai muka ki saboda muna ganin an samu man fetur sai muka kulle idonmu daga abubuwa kamar gemstone, gwalagwalai da abin da ya shafi harkar gona.
Ya ce, a halin yanzu duniya tana nesa-nesa daga man fetur tana komawa abin da ya shafi wasu makamashi musamman ganin yadda fetur ke kara ta’azzarar karuwar dumamar yanayi.
A jawabinsa, shugaban kamfanin MinDiber, Injiniya Sallim Salaam ya ce, an shirya taron ne domin mika jinjina ga ‘yan Nijeriya da suka koya tare da kwarewa wajen kera gwala-gwalai, irin gwalagwalan da za su yi gogayya da irin wadanda ake kerawa a kashen duniya.
Ya ce, taron ya kuma zama fagen da wadanda suka samu horon za su baje kolin irin kayayyakin da suka kera domin duniya ta gani, ya kuma yaba da irin kokarin su a wannan fagen.
A kan haka ya kuma mika godiyarsa ga babban sakataren ma’aikatar ma’adanai a kan irin goyon bayan da suka samu wajen samun nasarar bikin baje kolin ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa wa matasa don su bunkasa rayuwarsu.
Ya kuma nemi matasan da suka samu horon su koma jihohinsu domin su horars da wasu matasan, ta yadda suma za su samu abin dogaro da kai.
A nata jawabin, babbar sakatariyar ma’aikatar ma’adanai, Dakta Mary Ogbe, ta yi kira ne ga gwamnonin jihohi su tallafa wa matasan da kudaden da za su fadada harkokinsu tare da kuma horas da wasu matasan. Ta haka za a tabbatar da an hau hanyar yaki da talauci da zaman kashe wando a tsakanin matasan Nijeriya.
Taron ya samu halartar manyan ma’aikatan gwamnati, masu ruwa da tsaki a bangaren ma’adanai da sauran al’umma, inda suka yaba da irin ayyukan da matasan suka gabatar.
Daga cikin matasa 96 da suka fara horon matasa 36 ne suka samu nasarar kammala horon. Daya daga cikin matasan mai suna Felicitas Ella daga Jihar Kros Ribas ta mika godiyarta ga kamfanin da ya dauki nauyin horars da su ta kuma yi alkawarin aiki da abin da ta koya yadda kamata ta kuma yi alkawarin horas da wasu matasan a jihar su.