• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Diphtheria: Kano Ce Kan Gaba A Yawan Masu Dauke Da Cutar Mashaƙo A Nijeriya

by Muhammad
2 years ago
Diphtheria

Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Nijeriya ta ce cutar mashako (diphtheria) ta kashe mutum 80 a kasar daga watan Mayu zuwa Yunin bana.

BBC ta rawaito cewa, wani rahoton da hukumar ta fitar ta ce yanzu mutum 836 suka harbu da cutar kuma jihar Kano ce ta fi yawan wadanda suka kamu da ke da mutum 819.

  • Diphtheria: Mutane 123 Sun Kamu, 38 Sun Mutu A Jihohi 4 – NCDC
  • Diphtheria: Mutum 3 Sun Rasu, An Kwantar Da 7 A Asibiti A Kaduna

Hukumar ta ce alkaluman sun shafi kananan hukumomi 33 na jihohi bakwai da suka hada da Yobe da Katsina da Sokoto Zamfara da Kaduna da kuma Abuja.

Ko a makon nan an bayar da rahoton mutuwar yara kusan 10 sakamakon cutar a jihar Kaduna.

”Ana cikin babban tashin hankali”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

Tsohon shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Nijeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC Hausa cewa halin da aka tsinci kai a ciki abun tashin hankali ne, ba na wasa ba.

Ya ce dole ne a tashi a dauki mataki, idan kuwa ba haka ba za a ji kunya.

”Ina mamaki kwarai, tunda bai kamata a ce ana yi wa yara rigakafin wannan cuta tun farko amma kuma ana samunta ba, abun ma da muke gani da ke tabbatar mana da cewa an gaza ne wajen yin rigakafin ko kuma wasu ba sa kai ‘ya’yansu a musu rigakafin shi ne kaso 80 ba a musu rigakafin ba.”

Ya ce wannan babbar gazawa ce da ke nuna ya kamata gwamnati da hukumomi su tashi su yi wa kansu kiyamallaili.

Farfesa Abdussalam Nasidi, ya kara da cewa a halin da ake ciki, idan har mutum ya kamu da cutar to ba lallai ne rigakafin ya yi aiki a kansa ba, ballantana da a yanzu haka ana fama da karancin rigakafin shi kansa.

Yadda cutar ke kama mutum

Masanin ya bayyana wa BBC cewa cutar mashakon, na kama makogaro ne, ta hana mutum sakat.

Ya ce: ”Idan ta kama mutum za ta rike masa wuya kamar an shake ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne Ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babban barazana ce”

Likitoci sun ce hanya daya ta kauce wa kamuwa da cutar mashako ga manya da kananan yara ita ce yin allura saboda za ta kashe kwayoyin cutar da ke jikin mutum.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Diphtheria
Manyan Labarai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa
Manyan Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Next Post
Manhajar ‘Threads’ Da Yadda Ake Amfani Da Ita

Manhajar 'Threads' Da Yadda Ake Amfani Da Ita

LABARAI MASU NASABA

Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Diphtheria

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.