Matashin ɗan wasa Djed Spence ya zama zakaran gwajin dafi a matsayin Musulmi na farko da ya taɓa buga wa babbar tawagar ƴ anwasan Ingila wasan ƙwallon ƙafa a tarihin ƙasar.
Ɗanwasan bayan na ƙungiyar Tottenham ya buga wa tawagar ƴ an ƙasa da shekara 21 wasa sau shida, amma wannan ne karon farko da aka kira shi babbar tawagar da ta buga wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.
Duk da cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ba ta adana bayanan addinin ƴ anwasanta, an fahimci cewa Spence zai iya zama Musulmi na farko da ya buga mata wasa Djed Spence ya ce abin alheri ne abin murna. Domin ya rasa ma kalaman da zai bayyana irin farin cikin da ya shiga lokacin da aka gayyace shi domin ya je ya wakilci ƙasar Ingila.
- Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa
- Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo
“Ina yawan yin addu’a. Ina gode wa Allah a lokutan da nake cikin ƙunci.
Na yi imanin cewa Allah yana tare da ni a kodayaushe. Wannan muhimmin abu ne a wurina, da addinina.” In ji Djed Spence.
Tottenham ta tura ɗanƙwallon wasan aro har sau uku zuwa ƙungiyoyin
Rennes, da Leeds, da Genoa a baya kuma a sakamakon haka ɗan wasan ya samu ƙwarewa da gogewa sosai.
Spence ya ce ba ya jin wani ƙarin nauyi saboda addininsa, amma yana fatan rawar da zai taka a tawagar za ta ƙarfafa wa sauran ƴ anwasa masu zuwa gwiwa domin cika burikansu.
Kafin 15 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, minti 64 kacal Spence ya buga a gasar Premier League a kakar 2004 zuwa 2025. Bayan haka ne kuma ya buga minti 90 sau 19 cikin wasanni 22 da ya buga wa Tottenham.
Sauyin da ya samu mai girma ne sosai. Da farko, tsohon mai horarwa Ange Postecoglou bai ma saka shi cikin tawagar ƙungiyar da ta buga gasar zakarun Turai ta Europa ba har sai da aka kai zagayen ƴ an 16 kafin ya buga minti 180 a wasan da suka doke AZ Alkamaar.
Sai kuma lokacin da ya shiga daga benci wasan ƙarshe da Tottenham ta doke Manchester United domin ɗaukar kofi karon farko cikin shekara 17, wanda ya ba su damar zuwa gasar Champions League. Bayan buga wa Tottenham kowane minti a kakar wasa ta bana, Spence ya samu kira daga mai horarwa Thomas Tuchel, kociyan tawagar Ingila wanda ake sa ran zai jagorancin ƙasar zuwa gasar cin kofin duniya na 2026 da za a buga a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Meɗico.
Ɗan wasan ya ce “Tabbas abu ne muhimmi mutum ya samu damar buga wa Ingila wasa kuma kociyan tawagar ya tarɓe ni da kyau, kowa ya ba ni kyakkyawar tarɓa yadda ya kamata.
A watan Maris na shekarar 2022 ne ya fara buga wa ƴ an 21 wasa. A lokacin mai koyar da yanwasan Lee Carsley ya so ya gayyaci Spence gasar European Championship ta ƴ an ƙasa da shekara 21, amma sai rauni ya hana shi zuwa.
Lee Carsley ya taɓa faɗa wa shashen Hausa na BBC a farkon shekarar nan cewa: “Yana da ƙwarewa a fannoni; yadda yake jawo ƙwallo kuma ya yanka abokan hamayya, yake cin ƙwallon, yake tarewa. Ɗanwasa ne da ba shi da iyaka nan gaba.”
Kawo yanzu dai fatan da Djed Spence zai yi shi ne ya ci gaba da ƙoƙari har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana domin hakan ne kawai zai sa kociyan tawagar ta Ingila Thomas Tuchel ya gayyace shi zuwa gasar cin kofin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp