• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
in Labarai
0
Dokar Hana Sayar Da Burodi Mara Shaida, Litar Mai Fiye Da 50 Ta Tabbata A Zamfara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu a kan dokar da ta haramta sayar da burodin da ba a lika takardar shaidar inda ake yin sa ba, tare da jigilar sa a buhu.

Haka kuma an haramta sayar da man fetur fiye da lita 50, haka ma an haramta motoci masu gilashi mai duhu a duk fadin Jihar Zamfara.

  • Abubuwan Da Za Su Taimaka Wa Mai Azumi Ya Kasance Cikin Koshin Lafiya
  • Kula Da Fata Mai Maiko Da Ke Bata Kwalliya

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ta ce dokar mai lamba 02 da mai lamba ta 04, 2024 za ta taimaka wajen magance wasu matsalolin da ke taimakawa ga matsalar tsaro a jihar. Jiya Talata ne Gwamnan ya sanya hannu a dokar a gidan gwamnatin jihar da Gusau

Kakain Gwamnan ya ce, an sanya dokar ne sakamakon hare-haren da ake kai wa wasu al’ummomi a sassan jihar.

“Sakamakon hare-haren da aka kai wa al’ummomin wasu Kananan Hukumomin jihar nan, musamman Zurmi, Shinkafi, Kaura Namoda da Talata Mafara, tare da samun karuwar kai hare-hare da sace mutane a wasu yankuna da manyan hanyoyin jihar.

Labarai Masu Nasaba

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

“Gwamna Lawal ya sanya hannu a dokar No. 02 2024, wacce ta haramta sayar da biredi mara takardar shaida, tare da sanya biredin a buhuna, an kuma haramta wasu ayyukan da ba a amince da su ba a jihar.

“Wajibi ne duk gidajen biredi su sanya takarda mai dauke da cikakken adireshin kamfanin, tare da bayanan ayyukan da su ke aiwatarwa, ana so su yi wannan cikin gaggawa.

“Kada wani gidan man fetur ya kuskura ya sayar da fiye da lita 50 ga kowace mota a lokaci guda. Daga yanzu kuma, gidajen mai za su sayar da mai ne tsakanin karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

“Sayarwa ko yawo da biredi, yanzu zai zama kawai a Hedikwatar kowace Karamar Hukuma: Amma a Gusau, an amince a sayar a yankunan: Hanyar Damba—Zaria; Gada Biyu—Sokoto; Command Guest House a hanyar Kauran Namoda; Gusau Garage—Dansadau.”

Haka kuma dokar ta No. 04, 2024, wacce Gwamnan ya sanya wa hannu, ta haramta motoci masu dauke da gilashi mai duhu a Zamfara. “Haka kuma an haramta wa masu motoci rufe lambar motocin su a yayin da suke tafiya.

“Wajibi ne duk masu motoci su kasance tare da cikakkun takardunsu, sannan su bi dokar kiyaye dokokin hanya ta jihar Zamfara mai lamba No. 2, 2015, ko duk wata doka da ta shafi wannan.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Magidanta, Samari Da ‘Yan Mata Za Su Daidaita Rayuwarsu A Azumin Bana

Next Post

Omokri Ya Caccaki Peter Obi: Kar Ka Tayar Da Husuma A Nijeriya Saboda Ka Fadi Zabe

Related

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
Ra'ayi Riga

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

5 hours ago
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci
Labarai

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

7 hours ago
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
Noma Da Kiwo

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

8 hours ago
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje
Labarai

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

9 hours ago
GORON JUMA’A 09/05/2025
Labarai

GORON JUMA’A 09/05/2025

10 hours ago
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 
Labarai

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

11 hours ago
Next Post
Omokri Ya Caccaki Peter Obi: Kar Ka Tayar Da Husuma A Nijeriya Saboda Ka Fadi Zabe

Omokri Ya Caccaki Peter Obi: Kar Ka Tayar Da Husuma A Nijeriya Saboda Ka Fadi Zabe

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

May 9, 2025
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

May 9, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 9, 2025
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.