Dokar kayyade tsadar bukukuwan aure, zanen suna, kaciya da makamantansu a Sakkwato ta tsallake karatu na biyu a Majalisar Dokokin Jihar.
Wannan ya biyo bayan gabatar da kudurin dokar da Honarabul Abubakar Shehu Shamaki (APC- Yabo) ya gabatar tare da gudunmuwar Honarabul Faruku Balle (PDP- Gudu) a zaman Majalisar Dokokin a yau.
- An Bude Bikin Anime Na Kasa Da Kasa Karo Na 18 A Hangzhou
- Yadda ISWAP Ta Kai Hari Sansanin Sojoji, Mutane Da Dama Sun Mutu A Jihar Borno
Da yake gabatar da dokar, Honarabul Shamaki, ya bayyana cewar dokar na da manufar kayyade da takaitawa daidai gwargwado kan tsada da sharholiya da ake yi a bukukuwan aure, zanen suna da kaciya a Sakkwato.
Ya ce ko shakka babu dabi’ar almubazzaranci da ake yi da sunan bukukuwa ba karamar illa ba ce wadda ke haifar da tabarbarewar tattalin arziki a cikin al’umma.
“Wannan bakar dabi’ar idan aka ci gaba a haka ba tare da daukar mataki da kayyadewa ba, za ta sa aure ya yi wa jama’a matukar wahala wanda hakan zai iya haifar da zina, madugo, luwadi da sauran ayyukan assha,” In ji shi.
Dan majalisar ya kara da cewar a yanzu haka kasawar ango ga yin hidimar da aka bukata da sharholiya a yayin aure na haifar da watsewar auren baki daya.
“Matsalar ta haifar da yawaitar mace-macen aure a cikin al’umma. Don haka idan wannan dokar ta tsallake aka sa mata hannu a matsayin doka, za ta taimaka kwarai wajen rage tsadar aure da sharholiyar da ake yi da takaita yawan zawarawa,” ya bayyana.
A kan wannan Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Honarabul Aminu Achida, ya bukaci jin ra’ayin ‘yan majalisar wadanda baki daya su 30 suka aminta da karatu na biyu na dokar wanda a bisa ga wannan ya tura kudurin dokar a gaban kwamitin majalisa kan Harkokin Addini domin daukar matakin doka na gaba.