Tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai daga mazaɓar Ungogo/Minjibir a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Honarabul Bashar Aliyu Sambauna, ya soki matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.
Sambauna ya bayyana cewa wannan yunƙuri ne na tauye dimokuraɗiyya da karya dokar ƙasa.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
A wata sanarwa da ya fitar, Sambauna, ya ce tsarin mulkin Nijeriya bai bai wa shugaban ƙasa ikon tsige gwamna ba, don haka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da kuma rushe majalisar dokokin jihar babban kuskure ne da ya saɓa wa doka.
Ya ce, “Babu wani sashe a kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya bai wa shugaban ƙasa ikon cire gwamna ba bisa ƙa’ida ba.”
Ya yi ɗauraya game da irin wannan lamari, yayin da aka ayyana dokar ta-ɓaci a Jihohin Borno, Yobe da Adamawa a 2013 ƙarƙashin mulkin Goodluck Jonathan, ba a dakatar da gwamnonin jihohin ba.
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a.
Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”.
Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da ikon rushe zaɓaɓɓun shugabanni na jiha.
Bugu da ƙari, Sambauna ya caccaki yadda Gwamnatin Tinubu ke nuna bambanci wajen raba wa matasa tallafi.
Ya ce: “Seyi Tinubu ya bayar da kayan abinci a Arewa a matsayin tallafi, amma a Kudu yana bayar da tallafin kuɗi domin mutane su dogara da kansu wajen bunƙasa kasuwanci. Wannan nuna bambanci ne da bai dace ba.”
Amma, ya buƙaci gwamnati da ta girmama doka da ƙa’idojin dimokuraɗiyya, inda ya ce wannan mataki na Tinubu babbar barazana ce ga mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp