Sabon shugaban rundunar sojojin Burtaniya ya yi imanin cewa dole ne sojin Kasar su kasance a shirye don ‘yaki kuma da nasara’, yayin da yake tsokaci kan yakin da ake ciki a Turai Tsakanin Rasha da Ukraine.
Da yake magana kan wani hari da Rasha takai a Ukraine, Janar Sir Patrick Sanders, babban hafsan hafsoshin sojojin Kasar, ya yi gargadin cewa dole ne sojojinsa su kasance cikin shirin tunkarar yaki da zaluncin shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Ya kara da cewa, dole ne sojojin Burtaniya su zama cikin shiri, da zarar kungiyar NATO tayi kira su amsa kira don Yaki a gabashin Kasashen NATO.
Da ma dai tuni ya ankarar da rundunarsa Maza da Mata da su sake yin shiri don yin yaki a tarayyar Turai.
Akalla fararen hula 28 ne suka mutu a hare-haren Rasha a ranar Litinin, a wani harin makami mai linzami da aka kai kan wata cibiyar hada-hadar jama’a.