Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewar dole ce ta sanya gwamnatinsa raba kayan abinci ga wadanda matsalar Boko Haram ta shafa a jihar.
Ya ce yayin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kan raba abincin ga mabukata marasa karfi, ana kuma samun ci gaba wajen inganta rayuwar jama’a.
- Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana A Ciki (1)
- Kurakuren Da Ma’aurata Ke Tafkawa?
A cewarsa kayan abincin da yake rabawa na taimakawa wajen ceto rayuwar jama’a wadanda matsalar tsaro ta ɗaiɗaita a jihar
Yayin da yake tsokaci ga manema labarai a Gajiram da ke karamar hukumar Nganzai, Zulum ya bukaci samar da yanayin da zai dore wajen kula da lafiyar jama’a, maimakon tallafin da ake ba su lokaci zuwa lokaci.
Gwamnan ya yi watsi da zargin cewar tallafin na mayar da jama’a dogara da gwamnati, yayin da ya yi nuni da ayyukan da gwamnatinsa ke yi wajen inganta bangaren noma.
Akalla mutane 25,000 ne suka suka samu irin wannan tallafin da ya kunshi kudi Naira miliyan 25 da kuma kayan abinci.
Zulum ya kuma bayyana cewar jihar ta karbi tallafin abincin da ya kai buhu 15,000 daga hukumar da ke raya yankin Arewa Maso Gabas, wanda tunj gwamnatinsa ta raba wa mabukata.