Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya fitar da wata sanarwa mai ƙarfi game da yiwuwar dawowar wasu shugabannin siyasa cikin jam’iyyar. A lokacin ganawar da manema labarai a Kano, Abbas ya bayyana cewa APC ba za ta karɓi mutane da hukumomin yaƙi da cin hanci kamar EFCC da ICPC ke bincike ba.
Wannan sanarwa ta zo ne a yayin da jita-jita da ake cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar NNPP, musamman waɗanda ke cikin rukuni na Kwankwasiyya, suna duba yiwuwar komawa APC.
- El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci
- NNPP Ta Mutu, Kwankwaso Zai Sake Dawowa APC – Ganduje
Abbas ya bayyana cewa duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar dole ne ya nemi afuwa daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, bisa maganganun cin mutunci da aka yi a baya akan su da jam’iyyar.
Masu fashin baƙin siyasa na ganin cewa wannan magana ta Abbas tana nufin shugaban Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake zargin yana cikin tattaunawar yiwuwar sauya sheƙa. Wannan furucin na shugaban APC na Kano ya janyo muhawara game da yadda siyasa da daidaiton ra’ayi za su iya faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp