• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Matasanmu Su Rungumi Kasuwanci Na Zamani – Firdausi Dahiru

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
1 year ago
Kasuwanci

A wannan makon mun kawo muku wata matashiya da ta yi nisa a harkar kasuwanci zamani da aka fi sani da meta-force. A wannan hirar da ta yi da wakiliyarmu, ta yi bayani dalla-dalla yadda ta samu kanta a wannan sana’ar da irin nasarorin da ya samu. Ga dai yadda hirar ya kasance.

 

Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?

Sunana Firdausi Dahiru wacce aka fi sani da (Ummu Anas), an haife ni a Zariya a nan na taso na yi makarantar firamare da Sakandire yanzu haka a nan nake zaune

 

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Shin Firdausi matar aure ce?

Ni matar aure ce da ‘ya’yana biyu duka maza. Ni yar kasuwace, a da na yi kasuwanci sayar da leshina, atamfofi, kayan kicin, da kayayyakin gyaran jiki namu na mata wanda a yanzu babu kasuwancin da nake yi face Kirifto wato (meta-force).

 

To fa! mene ne kuma meta-force?

‘Meta-force decentralised world global’ business ne da talakawa da masu kudi kowa zai iya shiga a dama da shi, kuma network marketing ne wanda ake saka Naira zuwa Dala a yi rigista kuma kowa zai iya yi yaro ko babba, hatta jaririn da aka haifa yau za’a iya saya masa wannan hannun jari saboda idan ka yi rijista a nan take za su baka cash back token dinsu wato (TR coin). Wani abin farin ciki duk wanda ka gayyata ya zo ya sayi hannun jarinsu nan take za su biya ka dari bisa dari na abin da ya sa wani abin farin ciki nan take za ki cire kudinki kuma Daloli ne. To ta nan jama’a da dama sun fita daga kangin damuwa da talauci da suke ciki. Meta-force ya yi shekara uku da farawa wanda a yanzu wannan kasuwanci wasu sun gina gida, biyan kudin makarantar yara, abinci, aikin Hajji da sayen fili. Gaskiya wannan kasuwanci muna yi masa lakabi da Arziki Daga Allah, don duk wani abu da ya gagare ki kika fara In Sha Allahu komai ya zama tarihi da yardar Allah wannan abin sai kin fi karfinsa.

 

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?

Abin da ya ja hankalina da har na fara wannan kasuwanci na meta-force shi ne, akwai wani Iftila’i da ya same ni wanda na yi asara sosai, na rasa jarin da nake juyawa har da dukiyar jama’a a gaskiya na shiga tashin hankali sosai don bani da yadda zan yi na biya wadannan miliyoyin kudin. Cikin rahama ta ubangiji sai na ji labarin meta-force a ranar na yi register lebel 1&2 na fara ganin alheri da na samu a cikin satin sai da na tafi lebel 5, wanda a yanzu mun yi nisa Alhamdulillah a cikin kankanin lokaci na samu na fara biyan kudin da ake bina har na kammala na gode wa Allah Subhanahu Wata’ala.

 

Matakin karatunki fa?

Matakin karatuna ina da HND a ‘Dental therapy’ wanda na kammala Serbice tun 2017

 

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?

A gaskiya na fuskanci kalubale da dama wanda shi wannan kasuwanci yana son wayarwa da mutane kai su sanshi to a shekarun baya duk wanda na ba labari sai ki ji ana ce mana mayaudara ai karya ne, ko kuma guduwa za su yi ko wasu su zage ni abin ya batamin rai kamar zan bari, sai kuma wata zuciyar ta ce min ki ci gaba za ki ci nasara na sha wahala sosai tukunna kafin wasu suka fahince ni. Alhamdulillah yanzu ba kamar da ba saboda jama’a sun gane meta-force da wuya ki shiga Facebook, tiktok, Instagram ba ki ga ana tallan sa ba

 

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?

Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, shi ne a koda yaushe nake fadi idan na tuna ina cikin wannan kasuwanci kuma na shige shi a lokacin da ya kamata saboda na samu nasarori da dama abin da na mallaka ban taba tunanin ko a mafarki zan mallake su ba sai gashi a yau cikin kankanin lokaci Allah ya cika min burina ina rufawa kaina asiri da taimakon mutane duk a cikin wannan kasuwanci nake samun kudin, ai babu abin da zance wa wannan kasuwanci sai godiya da fatan alkhairi da addu’ar wanda ya kirkiri wannan kasuwancin Allah ya taimake shi Allah ya kara daukaka mana wannan kasuwancin namu.

 

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?

Abin da yake farantamin rai game da sana’ata ta meta-force shi ne yadda mutane suke min addu’a da fatan gamawa da iyayena lafiya da yi wa zuri’ata addu’an shiriya saboda tsananin jin dadi da suka yi suna samun kudade masu yawa wallahi ina matukar jin dadi kuma yana kara saka ni jajircewa da dagewa wurin kawo mutane, burina kowacce mace itama ta kasance cikin farin ciki kamar yadda nake ciki.

 

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?

Akwai hanyoyi da dama da nake bi wajen tallata kasuwancina kamar ta hanyar sadarwa irinsu WhatsApp, Facebook, tiktok, gidan biki, gidan suna ko cikin mota na hadu da wacce na sani zan ba ta labarin meta-force to ta haka ne nake tallatawa.

 

Dame kike so mutane su rika tunawa dake ?

Abin da nake so mutane su rinka tunawa da ni shi ne idan suka shiga wannan kasuwanci za su samu kudin da za su yi maganin damuwarsu to duk wanda ya tuna ni ce na yi silar sanar da shi zai min addu’a da ni da zuri’ata saboda na zama masoyiyarsa ta hakika ba zai taba mantawa da ni ba har abada.

 

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan umanki?

Ina samun goyon baya sosai wurin mahaifiyata a koda yaushe tana yi min addu’a kullum addu’arta Allah ya sa albarka a ciki ya yi min daukaka.’ Yan uwana suma suna yi min addu’a da fatan alheri. Eh Suma kawaye haka duk da ban cika yawan kawaye ba amma aminan amana suna yi min addu’a da fatan alheri kuma ina jin dadi matuka.

 

Me kika fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Na fi son natibe wear (dogwar riga) sai riga da siket da Abaya Shawaran da nake so na ba wa ‘yan uwana mata don Allah ku tashi ku yi sana’a komai kankantarta, ki dogara da kanki kada ki tsaya sai an yi miki ni tarihin sana’ata tun ina firamare kafin na yi aure ina saida Iloka, Kantun Gana, Aya, Dankunne, Spices a dakin kwananmu na makaranta, hatta handout bana Jira zuciyar ta nema ce sai dai na saya. To don Allah kada mu ce ai dole sai miji ya yi abu kaza amfanin nema kenan ke da ‘ya’yanki a gan ku tas gwanin sha’awa ko a dangi irin karramawa da za’a yi miki daban ce saboda ba ki zama ‘yar maula ba, komai kanwantar sana’a ki nemi albarkar abin Allah sai ya taimake ki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Next Post
Amfanin Zogale 18 Ga Lafiyar Jikin Dan’adam

Amfanin Zogale 18 Ga Lafiyar Jikin Dan’adam

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.