Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya yi kira ga tsofaffin ‘yan siyasa tsararrakinsa da su kauce don bai wa matasa dama a siyasar 2027.
A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, Bafarawa, wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar PDP, ya ce, “ba rikici nake yi da PDP ba. Mutane suna tunanin siyasa kawai takarar muÆ™ami ce, amma siyasa ita ce hidimtawa al’umma.”
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Babu Wanda Zai Ci Nasara A Yakin Cinikayya Ko Yakin Harajin Kwastam
- DSS Ta Maka Mahdi Shehu A Kotu Kan Zargin Ta’addanci
Ya bayyana cewa ya shafe kusan shekara 48 a siyasa, kuma yana da niyyar karkata hankalinsa zuwa ga inganta Nijeriya, musamman yankin Arewa, domin yana da shekaru 70 yanzu.
Bafarawa ya ce ya kafa ƙungiyar Northern Star Youth Alliance don haɗa kai tsakanin matasa Musulmai da Kirista domin samun ci gaba.
Ya kuma yi nuni da cewa zai iya mara wa ɗan takarar da ya dace baya, ba tare da duba jam’iyya ba.
A cewarsa, “Dole mu bai wa matasa dama su gwada kansu. Ai Janar Yakubu Gowon ma ya zama shugaban Æ™asa yana É—an shekara 30.”