Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan dakarun sojin Nijeriya 16 a Jihar Delta.
Manyan jami’an soji hudu da kananan sojoji 12 aka kashe a lokacin da suke kokarin sasanta rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli a jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Bayan Garkuwa Da Shi A Jihar Bauchi
- BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 1
“Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin kasa sun samu amincewa ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a mummunan aiki da aka yi kan al’ummar Nijeriya,” In ji Tinubu.
Tinubu ya bayyana hakan ne sa’oi bayan labarin yadda wasu sojoji suka cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna yankin suka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.
Mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da harin kan yankin na Okuama.
Sai dai ya jaddada cewa dole ne sojoji su kwato makaman da aka sace daga hannun sojojin da aka kashe.