Rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) ta yankin gabashin kasar ta shirya sojojinta na kasa, da na ruwa, da na sama da na harba makamai masu linzami, domin gudanar da atisaye mai taken “Joint Sword-2024B” a mashigin tekun Taiwan da arewa, da kudu da gabashin yankin tsibirin Taiwan.
Da farko dai, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da babban yankin ya sha nanata cewa ba zai iya ballewa ba, kuma dukkan wasu batutuwa da suka shafi tsibirin, batu ne na cikin gidan Sin. Amma wasu aikace aikace da bangarori masu adawa da dunkulewar baki dayan Sin wuri guda suke yi, wani yunkuri ne na takalar kasar Sin da keta cikakken ikon da take da shi kan yankunanta.
- Ko Za A Kore Ni Daga APC Ba Zan Daina Fadar Gaskiya Ba – Ndume
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Mataimakiyar Gwamna Ta Yi Kira A Guji Tarzoma A Rungumi Zaman Lafiya
Babu wata kasa a duniya da za ta amince da irin takalar da ake yi wa kasar Sin don gane da batun Taiwan, don haka, matakan da Sin ke dauka sun zama wajibi domin bangarori masu ruwa da tsaki su farga, kuma su gane cewa Sin ba za ta nade hannu tana kallo ana keta cikakken ikon da ‘yanci da muradunta ba.
Abin takaici ne yadda wasu ke nanata girmama manufar Sin daya tak, amma kuma suke nuna fuska biyu ta hanyar goyon bayan ‘yan awaren Taiwan, wanda kuma abu ne da Sin ba za ta lamunta ba.
‘Yancin Taiwan na nufin tashin hankali a Taiwan. Ya kamata mahukuntan yankin Taiwan da suke ganin suna samun goyon bayan wata babbar kasa, su nutsu, su yi nazarin yankuna irin nasu da aka yi ta ingizawa su nemi ‘yanci, shin yanzu a wani hali ko yanayi suke ciki? Duk wanda ke kaunar ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin, to ba zai goyi bayan ‘yancin Taiwan ba, sai dai idan yana da wata manufa da ta sabawa hakan.
Don haka, tilas ne Sin ta rika tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, kuma ‘yan awaren da masu ingizasu su san cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa wajen daukan dukkan matakai domin kare cikakken ‘yanci da muradunta da burinta ba, wato ganin dunkulewar kasar wuri guda.(Fa’iza Mustapha)