Kwanan baya, Amurka ta kakkabawa wasu kamfanonin Sin takunkumi, abin da ke da alaka da matsayin da Amurka ke dauka na mai da kasar Sin abokiyar gaba ta takara. A idon ‘yan siyasar Amurka, babu wani abu dake cikin huldar kasashen biyu sai takara. To ko mene ne abun da Amurka take nema ta hanyar daukar matakin yin takara?
A farkon wannan wata, tsohon jami’i mai kula da aikin shiga tsakani a harkokin yankin tekun Indiya da Pacific na kasar Amurka, Kurt Campbell, ya hau kujerar mataimakin sakantaren harkokin wajen kasar Amurka. A matsayin wani masani kan batun kasar Sin, ya taba rubuta wani sharhi a mujallar harkokin kasashen waje wato “Foreign Affairs”, inda a ciki ya ce dole ne Amurka ta saka shinge ga kasar Sin a fannin kimiyyar zamani, don kiyaye fifikonta a wannan bangare.
- Sin Ta Kira Taron Tattauna Kan Rahoton Gwamnati
- Kasar Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Taimakawa Jarin Waje
Matsayin da wannan dan siyasar kasar Amurka ya dauka ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta dorawa kamfanonin Sin takunkumi, wato kiyeye fifikonta, inda ainihin burin da take neman cimmawa shi ne hana bunkasuwar kasar Sin.
Sin da Amurka sun kulla yarjejeniyar San Francisco a shekarar bara, bisa ruhin mutunta juna, da zama tare cikin lumana, da kara tuntubar juna, da hana ta da rikici tsakaninsu, da nacewa ga kundin tsarin MDD.
Ya kamata, Amurka ta dauki matakan da suka dace don aiwatar da yarjejeniyar San Francisco, kuma kada ta ci gaba da kuskurenta na neman hana bunkasuwar Sin, duba da cewa hadin kai shi ne hanya daya tilo ta amfanar bangarorin biyu. (Mai zana da rubutu: MINA)