A ranar Litinin 2 ga watan nan, gwamnatin Amurka ta sanar da sabon matakin kayyade fitarwa kasar Sin na’urorin latironi, har ma ta kara shigar da kamfanonin Sin kimanin 140 cikin jerin sunaye wadanda ta hana a shigar musu da wadannan kayayyaki daga Amurka. Ban da wannan kuma, ta tsoma baki cikin harkokin cinikayya dake tsakanin Sin da sauran kasashe.
Wannan ne karo na 3 da Amurka ta sanar da irin wannan mataki na kayyade fitarwa kasar Sin na’urorin latironi. Amma Amurka ba ta cimma burinta ba ko kadan.
- Majalisa Ta Dakatar Da Zama Kan Ƙudirin Dokar Haraji
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Shari’a Da Majalisa Su Yi Aiki Tare Kan Dokar Haraji
Cibiyar nazarin tsare-tsaren duniya ta Amurka ta CSIS ta gabatar da alkaluma dake nuna cewa, daga shekarar 2016 zuwa 2023, yawan kudin cinikin na’urorin latironi tsakanin Sin da kasashe kamar su Amurka, da Japan, da Holland da dai sauransu, ya karu a maimakon raguwa.
Ban da wannan kuma, CSIC ta ba da alkaluma masu nuna cewa, tun daga shekarar 2017, yawan kudaden da kamfanoni mafi girma 8 a kasar Sin masu kera na’urorin latironi suka kashe ya karu sosai, inda ya zuwa karshen shekarar 2022, saurin karuwar ya kai kashi 40% bisa na 2021, abin da ya bayyana cewa, Sin na gaggauta kirkiro na’urorin latironi don maye gurbin kayayyaki na Amurka.
Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, sana’ar samar da na’urorin latironi na matukar bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, kuma Sin tana mallakar kamfanoni masu samar da kayayyaki mafi yawa a duniya, inda ita kanta wata babbar kasuwa ce. Hakan ya sa, hadin kai da kasar Sin a wannan bangare ba shakka dole ne ake yi shi, kuma ya kasance wani bangare na tsarin samar da kayayyaki a duniya.
Alal hakika dai, duniya na dunkulewa a wannan bangare, amma matakin da Amurka ke dauka ya kawo cikas ga ciniki tsakanin kasa da kasa, kuma ya keta zaman oda da dokar kasuwa, har ma ya haifar da barazana ga tabbacin tsarin samar da kayayyaki a duniya. An yi hasashen cewa, kamfanoni da dama, ciki har da na Amurka a wannan bangare za su yi hasara.
Matsa lamba da Amurka take yi ba zai dakile ci gaban fasaha da kimiyyar kasar Sin ba. Bunkasuwa a wannan bangare na bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, ya kamata Amurka ta yi watsi da tunanin babakere, ta kuma rungumi hadin gwiwa, don wannan ita ce hanya mafi dacewa da za ta bi. (Mai zane da rubutu: MINA)