Wani matsashi haifaffen Jihar Gombe kuma kwararre a bangaren fasanhohin zamani, Nasir Bappi, ya kirkiri sabuwar manhajar ‘Unlock Arewa’ a yanar gizo.
Ya ce ya kirkiri manhajar ne don nuna wa duniya kyayawan al’adun Hausawa na gargajiya.
- Ƙarancin Wayewa da Samar Da Labaru Masu Kyau Ke Durƙusar Da Kannywood
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya(2)
Matashin ya ce ya bude manhajar ne don saukaka wa mutane wajen musayar fasahohi tare da habaka kasuwanci tsakanin juna, gami da kokarinsa na fito sa kyawawan al’adun gargajiya da suke arewa ga duniya baki daya.
Manhajar ta kunshi al’adun Hausawa har da abin da ya shafi masarautu da sutura da abinci da sauran abubuwan al’adar Malam Bahaushe. Sabuwar manhajar na dauke da al’adun garuruwan Hausawa daban-daban da ire-iren abincin da aka fi ci a wadannan garuruwa.
Ya ce babban burinsa shi ne taimaka wa mutane wajen yada kasuwancisu ta hanyar manhajar
Ya ce, “Na kirkiri manhajar ‘Unlock Arewa’ domin ya taimaka wa mutanenmu da suke arewacin Nijeriya.
Yadda na tsinci kaina a wannan fasahar shi ne lokacin da nake karatu a kasan waje bayan na karanci darasin ‘information technology’, bayan da na dawo Nijeriya shi ne na zo na bude kamfani mai suna ‘Unlock Arewa’.
“Dalilin da ya sa muka bude wannan manhajar shi ne mu saukaka wa mutane wajen musayan ra’ayoyi da abubuwa da yadda kuma matane suke kasuwanci, sannan da bunkasa al’adunmu da tarihinmu da abubuwan da suka kamata.
“Akwai masarautunmu da sarakunanmu, za ka ga yadda mutane ke cin abinci da yadda suke abubuwa, don haka a wannan manhajar mun yi kokarin kawo duk wadannan abubuwan domin sannu a hankali muna kokarin mantawa da al’adunmu da tarihinmu.
“Babban burina na bude wannan manhajar shi ne na taimaka wa mutane su samu ayyuka ta wannan manhajar da yadda za su ke tattaunawa da juna bayan haka kar su manta da al’adunsu ta hanyar suke karantawa domin sanin abubuwan da ke faruwa da wadanda suka faru.
“Babu yadda za a yi mu ci gaba ba tare da mun san bayanmu ba. Don haka muna bi gari-gari, kauye-kauye muna koyar da mutane kyauta.”
Ya ce a kalla zuwa yanzu sun koyar da mutane kusan 6,800 domin su kara samun ilimi na fasahar zamani kuma su taimaka wa kansu, “Daga gida mace za ta iya aikinta ta samu kudade ko na miji ya yi aikinsa daga gida ya samu kudadensa ba tare da a dogara da gwamnati ba.
“A cikin manhajar namu mutum idan ya duba zai ga kowace gari akwai masarautu daban-daban. Ni yanzu misali a ce ni dan Gombe ne ban san Masarautun Kano ba, ban san yadda suke al’adunsu ba, ban san wani irin abinci suke ci ba, sai dai kawai a ce Hausa /Fulani.
“To daga ka shiga ciki za ka ga kowace masarauta da yadda suke suna, yadda suke aure, yadda suke rayuwarsu, wasu irin sana’o’i suke yi, mutanen da suke harkar kiwon ne ko saka ne, ko me ye za ka samu a wannan manhajar.
“Muna son mu sanya arewa a tafin hannun mutane mu daukakata da al’adunta.
“Manhajar Unlock Arewa a yanzu muna da masu wakiltarmu a kasashe 32 wadanda suna taimaka wa matane kama daga neman guraben karatu, tallafin karatu, kasuwanci, misali kana son sayan kaya a China ba ka san waye za ka dogara da shi ba, shi wakilinmu zai taimaka maka hada da masu sayarwa har kayanka ya zo Nijeriya.
“Bayan haka kuma, a kowace kasa in kana bukatar abu ko in za ka je yawan bude ido ko wani abu za su taimaka maka su hada da kamfanin da ya kamata wanda ba za a cuceka ba kuma su maka bayanin abubuwan da za su taimakeka a wannan kasar.
“Na kirkiri wannan manhajar saboda in nuna wa duniya kyawawan al’adunmu na gargajiya. Babban burina shi ne in hada arewa da duniya ta yadda za mu taimaka wa juna gabaki daya.”