Lauyoyin Godwin Emefiele, sun koka kan yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake kama shi bayan belinsa da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar.
Babban Lauyan da ke kare dakataccen gwamnan na CBN, Joseph Daudu, ya bayyana haka bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Talata.
- Kotu Ta Bayar Da Belin Emefiele Kan Miliyan 20
- An Gurfanar Da Emefiele A Kotu Kan Mallakar Makamai Ba Bisa Ka’ida Ba
A ranar Talata ne mai shari’a Nicholas Oweibo ya amince da bayar da belin Emefiele a kan kudi naira miliyan 20 sannan ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali har sai an cika sharudan belin.
Jim kadan bayan yanke hukuncin, jami’an DSS sun kafe motarsu kirar Hilux a bakin kotun, tare da sake cafke shi bayan sun ɗan yi hatsaniya da Jami’an Gidan Gyaran Hali (NCS) a kan wanda ya fi dacewa ya tafi da shi.
Wannan ne ya sa Daudu, Babban Lauyan Nijeriya (SAN), da sauran lauyoyin Emefiele suka yi kiran da a hanzarta bin abin da doka ta ce kan sake kama wanda suke karewa da DSS ta yi.
Hakan ne ya sa tawagar lauyoyin nasa suka fito wajen suka yi wa manema labarai karin haske kan lamarin.
DSS ta gurfanar da Emefiele a kotu da safiyar ranar Talata, kan tuhumar mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, zargin da shi kuma ya musanta.