Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta gudanar da wani samame tare da hadin guiwar sauran jami’an tsaro a jihar Kogi a ranar Lahadi, 26 ga Maris, 2023, inda rundunar ta kama wasu gungun masu aikata laifuka su shida a Gegu Beki, a Lokoja kan hanyar Abuja.
Mai magana da yawun hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadi ya ce, mutane shidan sun hada da kanal AU Suleiman (mai ritaya), Barista MK Aminu, Kabir Abdullahi, Isah Umar, Kadir Echi da Adama Abdulkarim.
Makaman da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindiga kirar famfo daya, kwalbasar alburusai 4, kwalbasar alburusai ta AK47 guda daya da jimillar kudi Naira N11,030.
Har ila yau, a ranar 25 ga Maris, 2023, jami’an sun kama wani matashi mai shekaru 20 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Haruna Adamu, a kauyen Fotta da ke karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.
Hukumar ta DSS ta ce, ta kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, kwalbasar alburusai daya da harsashi mai tsawon 7.62mm guda hudu daga hannun wanda ake zargin.
Haka kuma a ranar 23 ga Maris, 2023, an kama wani mai suna Aminu Ibrahim, wanda ake zargin dan bindiga ne a hanyar Kubwa Expressway, Abuja a lokacin da yake kan hanyarsa daga jihar Nasarawa don kai alburusai 432 mai girman 7.62 x39mm da aka boye a cikin galan din manja mai fadin lita hudu zai kai wa ‘yan bindiga da ke jihar Neja. An kuma karbo kudi Naira N21,400 daga hannun wanda ake zargin.
Hakazalika, a ranar 22 ga Maris, 2023, an kama Babangida Ibrahim, mai jigilar makamai zuwa ga ‘yan bindiga a jihar Zamfara a Bukuru a karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Filato.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsa sun hada da harsashi 468 mai girman harsashi 7.62 x 39mm da kudi naira N21,090.
Dukkan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu.