Wani rahoto da TRT ta wallafa a shafinta ya ce, Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce ta bankado shirin da wasu ke yi don bata sunanta da na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sakamakon tsare Godwin Emefiele, shugaban babban bankin kasar da aka dakatar daga aiki.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta ce jami’anta sun gano cewa wasu mutane da kungiyoyi na shirin gudanar da zanga-zanga a wasu sasan kasar da zummar “bata sunan” hukumar da gwamnati bisa “dakatarwa da kuma yin bincike kan Mr Godwin Emefiele.”
- Shin Dakatar Da Godwin Emefiele Zai Farfado Da Tattalin Arzikin Kasa?
- Kotu Ta Umarci DSS Ta Bai Wa Emefiele Damar Ganin Lauyansa Da Iyalinsa
“Wadannan kungiyoyi za su taru a sassa daban-daban na Abuja da Lagos a makonni masu zuwa dauke da kwalaye masu rubutun da ke nuna gwamnati a matsayin mara kyau sannan su yi kira da a saki Emefiele nan take,” in ji sanarwar da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar.
DSS ta kara da cewa tana sane da yadda aka dauki nauyin wasu mutane suke rubuce-rubuce da sharhi a soshiyal midiya da ma sauran kafafen sadarwa don cimma burinsu.
Ta kara da cewa ta gano masu son yin kutse cikinta don yin amfani da “ma’aikata bara-gurbi” da zummar bata sunan shugabanninta.