Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), a ranar Lahadi, ta kama Editan Sashen Pidgin na BBC, Adejuwon Soyinka, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), da ke Legas.
Soyinka wanda shi ne Editan Yankin Yammacin Afirka, an ruwaito cewa, an tsare shi a MMIA da ke Legas da misalin karfe 5:40 na safe a ranar Lahadi, 25 ga Agusta, 2024, jim kadan bayan isowarsa Nijeriya a cikin jirgin Virgin Atlantic daga kasar Ingila.
Sai dai an tattaro cewa, yunkurin jin ta bakin Soyinka ya ci tura, saboda kiran da aka yi masa da tura sakonnin a wayarsa, har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton babu amsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp