Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta damke jami’an banki a cikin batagari wadanda suka kware wajen sayar da sabbin takardun kudin da aka sauyawa fasali.
Da yake bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kakakin hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, ya ce wasu batagari daga cikin kungiyoyi na da hannu wajen sayar da sabbin kudaden da aka sauyawa fasali.
Ya kuma ce a cikin ayyukan hukumar ta DSS, sun tabbatar da cewa wasu ma’aikatan bankunan kasuwanci na taimakawa batagari wajen jefa ‘yan kasa cikin mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki.
Duk da cewa, kakakin hukumar ta DSS bai ambaci sunan wani banki ba ko kuma a jihar da lamarin ya faru, hukumar ta gargadi masu sayar da kudin da su daina wannan aikin jahilcin.