A yau shafin namu zai yi duba ne game da irin dokokin da samari ke sakawa ‘yan Matan da za su aura tun kafin aure.
Musamman idan muka yi duba da yadda wasu ‘Yan matan ba sa iya fita daga gidansu ba tare da sun tambayi samarin nasu ba, ko da kuwa tare da iyayensu za su fita, kasancewar ba su tambayi izinin saurayin ba.
- Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Ta Fara Raba Wa Manoma Kayan Adana Amfanin Gona -Sakatare
- Manchester United Ta Kafa Mummunan Tarihi A Watannin Oktoba
Haka kuma samarin na saka wa ‘yan matan doka cikin dokokinsu na hana fita dazarar la’asar ta yi, tare da dokar dora hotonsu a wasu gurare ko turawa kawaye, ko zuwa wasu gurare ba tare da neman izninsu ba, ko zuwa kwana gidan ‘yan uwa ko da kuwa ana biki, da sauran dokoki irin wanda matan aure ke bi.
Sai dai kuma wasu na ganin cewa saka dokokin na da matuwar amfani ga ‘yan matan, domin samu gyara musamman ta yadda zamani ya sauya a yanzu. Ta wani bangaren kuma wasu na ganin cewa saka dokokin ba hanya ce me bullewa ba, domin kuwa za a haifi da mara ido ne, ayi haihuwar guzma da kwance, uwa kwance, in ji masu iya magana, domin hakan zai kawo nakasu da ci baya cikin soyayyar wadda ba za ta kai ga aure ba.
A ganinsu hakan ba zai taba kawo gyara ba face tabarbarewar soyayyar. A cewar su saka dokokin alamomi ne da ke nuni da cewa; shi saurayin mutum ne me tsattsauran ra’ayi wanda in aka yi aure mace za ta kasance cikin kunci da takura.
Wasu samarin na saka dokokin ne saboda ra’ayin hakan da suke da shi, wasu kuma na sakawa ne saboda takama da tunkaho da nuna isa musamman cikin abokansu dan nuna musu cewa sun isa da wadda suke so, ko kuma su nunawa kowa cewa tsananin son da mace take masa ne ke sawa ta yi masa biyayya shi ba sonta yake sosai ba.
Wasu kuma tsananin so ne ke sawa su sakawa wadda suke so doka saboda kishinta da saurayin ke yi, na ganin kar wani ya rabeta. Wasu kuma suna saka dokokin ne sabida suna da tsarin hakan a ransu, tsanainsu ke sa su su yi hakan, wasu kuma suna sakawa ne sabida su gwada wadda suke so, su ga shin za ta iya yi musu biyayya bayan aure ko kuwa?, wani kuma ya ga abokinsa ya saka wa masoyiyarsa tana bi, shi ma ya kudurce sai ya saka wa tasa. Akwai dalilai da dama wanda ke sa samari masu saka doka saka dokoki ga wadda suke so.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta baki wasu daga cikin mabiyansainda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Kueen-Nasmah daga Jihar Zamfara:
To samarin da ke saka wa ‘yanmatan da za su aura dokoki, ya danganta daga ra’ayi. Wasu da yawa tsautsauran ra’ayi ne, wasu kuma kishi ne. Yana da amfani idan har an saka dokar yadda ya dace, dalili na kuwa shi ne; idan har ya kasance yarinyar tana da rawar kai to a kwai bukatar wanda take so ya rika kwabarta, domin idan har a kwai so to komai yana zuwa da sauki.
Akan kaina gaskiya bani da ra’ayin sakawa wanda nake so doka, domin yawan sa doka nasa mutum ya fita ranka, da a ce ni namiji ce ba zan tsaurara ba, haka idan ni ce aka sakawa doka zan auna dokar idan har akwai bukatar na yi biyayya zan bi, amma ba zan ce duk dokar da aka sa zan bi ba, dan wasu lokutan maza suna amfani da damar hakan ne su tauye ki musamman zaman inda muke ciki, amma idan har an yiaure dole na yi biyayya.
Shawara ta ga wanda suke cikin hakan shi ne; su rika auna umurnin da aka basu idan akwai bukatar su bi sai su bi wata rana dokar na da fa’ida.
Nana Aicha Hamissou Abdoulaye daga Maradi Janhuriyar Nijar:
Tsantsar soyayya ce take sanya maza saka wa ‘yan mata dokoki tun kafin aure. Wanda yake son mace yana kulawa da ita matukar gaya, kowanne lokaci yana so ya ji halin da take ciki.
Idan ta fita jininsa yana kan akai fa gudun wani ya kallar masa budurwa har ya yi masa sama da fadi. Shi ya sa suke yin kaffa-kaffa ta hanyar dokoki. Har ila yau dora hotuna barkatai a midiya ba karamin kalubale gare shi ba, ban taba ganin laifin namiji ba don ya dora wa mace wadannan dokokin ba, ila birgeni da ya yi saboda nuna kulawa ga abar kaunarsa.
Saka dokoki yana da matukar amfani, zai rage kalubalen da za su tun karo masoya bayan aure su hana su rawar gaban hantsi. Misali mace ba ta ba tacan, daga nan wani namiji zai iya ganinta har ya yi kokarin kawo mata farmaki.
Sai kuma masu dora hoto sun fi ma kalubale saboda hoto a yayin da yake cikin wayar mutum ne yake killace, da zarar ya fita zai zagaye duniya sosai idan mijin mace ya gani hakan zai haifar da matsala. Wasu kuma za su iya amfani da hoton su bata mutum, wasu kuma za su ji a ransu sai sun nemi macen sun so ta.
Ni Nana A’isha ina maraba da wadannan dokokin dari bisa dari, kuma ina ba wa duk wata ‘ya mace shawarar matukar saurayinta ya sanya mata wannan dokar ta bi sau da kafa saboda soyayya ce ta kawo haka. Wani saurayin da kan shi ma zai iya dora budurwarsa yana tallar ta da suna so, hakan kuma sam ba soba ne don alamu sun nuna babu kishi a tattare da shi.
Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Gaskiya abu ne mai kyau mudduun kasan an kuwa aura maka yarinya ta fara bin duk wata doka da ka saka mata shi ne daidai da ma shi kasan daura hoton ai ba wani abu ne mai kyau ba dole ka hana ta tun kan ku yi aure, yana da kyau kuma shi ne; ya tabbata kana kishin matarka, in ta bi to kasan ko aure ta ba ka da matsala da itain kuwa taki to ko kun yi auren da alama ba za ta bi dokar ka ba shi yasa suke farawa tun kan aure ya zo.
Yana da amfanin sosai, hakan zai sata san ita ma fa ta kusa shiga sahun wanda suke karkashin mazan su Insha Allahu kuwa ai mu muna kan bi ma, Mu bi umarni sahu da kafa domin biyayya abu ne mai kyau.
Ummu Maher (Miss Green) daga Jihar Kano:
Gaskiya abin da yasa wasu mazan suke haka ba komai ne yasa ba, saboda suna kishin ‘yan matan nasu, shi ne; yasa suke kafa musu dokoki, wanda a ganina bai dace hakan ba amman dole idan kana son mutum ka yi kishi, amman kada dokokin su yi yawa.
Gaskiya ba shi da amfani, dalili na shi ne; za kaga budurwar ta shiga cikin takura, a wani lokacin ma har da tsoron shi saurayin, wanda a ka’idance bai kamata hakan ba. Gaskiya duk daina matsayin mace idan ni na miji ce gaskiya ba ni da ra’ayin hakan. Gaskiya ba zan bi ba amman zan bi wasu indai ba su karya doka ba.
Gaskiya duk wanda ya tsinci kansa a cikin matsala irin wannani na ba shi shawara da ya yi hakuri kuma ya zauna da saurayin su magantu a kan hakan.
Yareema Shaheed Dan Amar daga Jihar Kano:
Duk namijin da yake sa wa matar da zai aura dokoki tun kafin su yi aure, to hakan na nunawa cewa yana kishinta ne kuma yana mutukar sonta, domin duk abin da mutum baya so to baya nuna kishinsa a kai.
Saka dokokin yana da matukar amfani, domin tun kafin ta shigo gidan mutum za ta koyi kiyaye dukkan abin da tasan mijin baya so, hakan zai sa su zauna lafiya cikin aminci idan sun yi aure. E! Nima zan sa wa wacce zan aura dokoki tun kafin mu yi aure, domin hakan zai sa mu fahimci juna tun kafin mu yi aure.
Ina ba wa wanda suka tsinci kansu ciki da su yi hakuri su ci gaba da bin dokokin wanda zai aurensu, domin yin hakan shi ne zai tabbatar da soda kaunar da suke yi wa juna nahar abada.
Raheenat Mamoudou daga Nijar Jihar Niamey:
A tunani na da kuma Nazari da na yi wa lamarin ba komai yasa suke haka ba illa son zuciya da kuma takurawa mutum saboda wani dalilin na su marar tushe, ni irin hakan ya taba faruwa da ni ba so daya ba kuma ba so biyu ba, na yi wani sauri ko kasuwa zan je ya dinga mita kenan balle har na tafi ba tare da na sanar da shi ba, magana babu irin wadda ba zai min ba, sai ki rantse shi ne mahaifina, idan kuma na je kasuwar kafin na dawo zai kira ni a kalla so goma ko fiye da hakan amma yanzu na bashi jan kati na kuma nuna mi shi ko gobe idan zai yi soyayya ya daina shinfida dokoki tun da ba a riga an daura fatiha ba.
Bai da wani amfani saboda yana janyo rashin jituwa tsakanin masoya, wasu saboda kishi su ke haka, wasu kuma kawai haka Allah ya halice su idan ka kuskura ka aure su bone ya cika saboda ko unguwa ka je sun dinga zarginka kenan Allah dai ya kyauta ameen.
Maganar gaskiya ba zan amince ba haka kawai ina dalili. Shawarata gare su shi ne su daina irin hakan babu kyau idan an amince da juna an wuce waje na dai na shinfida wasu dokoki mara kan gado ba a ka da a yi kishi amma a dinga yi ana nazari Allah ya samu dace ameen.
Rukayya Ibrahim Lawan:
Wasu mazan suna yin haka ne don suna jin cewa kamar sun isa da yarinyar da za su aura. A nufin su dole sai sun dora ta a dokokinsu tun a waje don su gwada karfin ikonsu. A gaskiya ba shi da wani amfani a ra’ayina domin kuwa hakan ba ya kawo gyara sai dai ya bata masa al’amarin soyayyarsa. Da sannu-sannu sai su fara samun rikici a tsakaninsu idan ba a yi Sa’a ba sai kaunar ta ruguje.
Sam! ba zan iya ba, don kuwa ba za ta sabu ba bindiga a ruwa. Idan namiji ne ya yi kokari ya dinga yi wa budurwarsa uzuri, ya sani cewa a matakin da suke ba hakkinsa da ya rataya a wuyanta. Idan mace ce ta yi kokarin lurar da saurayin nata ya jinkirta dokokinsa har zuwa lokacin da ya dace.
Bilkisu Musa Galadanchi Sokoto Nijeriya:
Saboda mace ta shirya ta sani fa cewar idan sun yi aure wadannan dokokin za su ci gaba har ma wanda suka fi su, za mu iya kiran wannan da yi wa tufkar hanci ba dan komai ba sai don tulin matsalolin da ka iya tasowa daga baya. Yana da matukar amfani sakawa din, a nan namiji zai kara tabbatar idan tashi za ta zo dai-dai da wacce yake shirin aura din.
Eh! kam saboda gwara in san wa nake tare da ita shin za ta yi mun biyayya bayan aure? Tabbas in har auren nake so, ai idan har auren gaske zan yi na san dole zan bi dokokin wanda ya ajiye ni. Shawarar da za a ba su shi ne su yi biyayya, su rufawa kansu asiri.