Dubban jama’a ne suka shiga jam’iyyar NNP a Jihar Neja, inda a yanzu haka wasu sama da 5000 suka mika sunayensu suna jiran a yi musu rajista.
Sakataren jam’iyyar, Kwamared M. K Garba ne ya bayyana hakan ga manema labaru a Minna.
‘Yan takarar majalisar wakilai goma da ‘yan takarar majalisar jiha ashirin da biyar ne zasu tsaya takara a babban zaben 2023 da ke gabatowa.
Ya ce, “Sakamakon hadewar kungiyar Kwankwasiyya da TNA ya kara wa jam’iy-yarmu tasiri da jama’a ke rububin shigowa, domin tafiyar siyasa bayan shekaru goma muna wanzuwa a matsayin jam’iyya. Ganin yadda jam’iyyar ke tasiri bayan mun kammala zabukan.
“Mun kafa kwamiti domin zauna wa da wadanda ba su samu nasara ba ta yadda za a tafi gaba daya, yanzu haka akwai ‘ya’yan jam’iyyun PDP da APC da ke kwara-rowa zuwa NNPP domin yin tafiya tare.
“Tsarinmu a NNPP shi ne, muna gayyatar jama’ar da ke hidimta wa al’ummomin-su da shigo dom mu yi aiki tare wajen kawo karshen rashin tsaro a jihar da kawo koma bayan da jihar ke samu.
“NNPP jam’iyyar aminci ce, burinmu kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, ta-lauci da jama’a ke fama da shi, yanzu haka ban da fom da aka aiko daga uwar jam’iyya ta kasa da ta jiha sama da miliyan goma muka yi wa rajista, kuma muna kokarin ganin dukkanin kujerun siyasa mun ajiye ‘yan takara domin ganin mun samar da canji a jihar.”
Kwamaret M. K ya ce akwai bukatar al’ummar jihar su tashi daga dogon baccin da suke yi wajen kawo sauyi da kuri’unsu.