• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dubban Mambobin Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Bauchi

A Bayyana Sunayen Wadanda Suka Fice Din - APC

by Khalid Idris Doya
3 years ago
PDP

Dan takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, Alhaji Adamu Dako tare da magoya bayansa sun ayyana ficewa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Da ya ke jawabi a lokacin yankan katin shiga PDP a ofishin jam’iyyar da ke karamar hukumar Bauchi a ranar Litinin, Dako ya bayyana cewar abubuwa ba su tafiya daidai a cikin APC don haka ne ya yanke shawarar ficewa.

  • Gwamnatin Legas Ta Rufe Wata Makaranta Saboda Mutuwar Dalibi
  • An Fitar Da Rahoton Nazari Game Da Yanayin Aiki Na Alummun Yankin Xinjiang

“Yau ni da magoya bayana sama da dubu bakwai (7,000) mun ayyana ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

“Na kasance a da baya jagora a cikin jam’iyyar APC, amma cikin ikon Allah na fice daga jam’iyyar sakamakon matsaloli da suke jibge a cikinta. Na yi nadamar bata shekara da shekaru a cikin jam’iyyar APC.”

Alhaji Dako ya ce, dukkanin alamun fadin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ya tabbata, yana mai cewa, hatta zabin da jam’iyyar ta yi wa dan takarar gwamnan Sadik Baba Abubakar alamu ne da ke nuna ba za ta iya samun nasara a zaben gwamnan jihar ba.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

“Wannan dan takara da jam’iyyar APC ta ayyana kalubale ne a gabanta a zaben 2023.”

“Duk wanda ya san yadda aka yi hadaka aka kafa APC, yanzu kowa ya san ba jam’iyya ake yi ba son zuciya kawai ake bi. APC ta mutu murus a jihar Bauchi. Na shigo jam’iyyar PDP da kyakkyawar manufa.”

Ya ce, sun shiga PDP ne lura da irin nasarorin da gwamnan jihar Bala Muhammad ya cimma na kyautata jihar.

Don haka ne ya nuna kwarin guiwarsa na cewa gwamna Bala zai sake samun nasara a karo na biyu tare da kiran al’umma da su mara wa gwamnan ba.

Da yake amsar wadanda suka sauya shekar, shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Bauchi, Alhaji Abdulkadir Alin Bababa, ya sanar da cewa, jam’iyyar ta karbi sabbin mambobin jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP su dubu bakwai.

Shugaban wanda ya samu wakilcin, mataimakinsa Sani Ahmad, tare da sauran shugabanin jam’iyyar a karamar hukumar, ya bai wa wanda suka dawo jam’iyyar tabbacin samun adalci daga wajensu tare da share musu hawayen matsalolin da suka zo da su, ya rokesu da su taimaka domin samun nasarar PDP a 2023.

Shi ma a jawabinsa na lale ga sabbin mambobin, babban mai bai wa gwamnan jihar Bauchi shawara kan harkokin siyasa, Hon. Abubakar Faggo, ya bayyana cewar yadda ake shigowa cikin jam’iyyar PDP alamu ne da ke nuna irin gamsuwa da salon mulkin gwamna Bala.

Ya ce, tabbas gwamna Bala Muhammad na gudanar da kyawawan ayyukan bunkasa jihar Bauchi, don haka ne ya nemi jama’ar jihar da su kara ba shi dama domin kyautata jihar, ya kuma nuna cewa tabbas wadanda suka dawo jam’iyyar za su samu goyon baya daga PDP.

Faggo, ya nuna cewa jam’iyyar APC bata kyauta wa mambobinta, don haka ne ma suke ta komawa cikin PDP.

“Mu a PDP akwai adalci, don haka kun zo lallai kuma za a muku adalci.”

Da ya ke maida martani kan wannan matakin, jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Adamu Aliyu Jalla, ya ce suna da ja man cewa mutum 7,000 sun fice daga jam’iyyarsu.

Ya ce, kowa na da ‘yancin sauya sheka, amma ya ce da dandazon mutum kaza fita wannan kuma akwai bukatar tabbatarwar kafin amincewa.

“Farfagandar siyasa ce kawai. Mutum 7000 wasa ne. Mu ba mu da bayanin cewa wannan adadin sun fita a jam’iyyunmu. Don haka muna kalubala tarsa da ya bayyana sunayen mutum 7000 din.”

Ya ce babu gaskiya na cewa ana gudanar da mulki cikin jam’iyyar APC bisa rashin adalci, ya nuna cewa suna da karfin da za su iya cin zaben 2023 tare da goyon bayan al’ummar jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
Siyasa

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
Siyasa

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Next Post
NCC Ta Bai Wa Kamfanonin Sadarwa Kwana 30 Don Warware Matsalolin Masu Amfani Da Layukansu

NCC Ta Bai Wa Kamfanonin Sadarwa Kwana 30 Don Warware Matsalolin Masu Amfani Da Layukansu

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.