Ƙungiyar Mata Network ta gudanar da taron ta na shekara-shekara karo na 6 a ƙarshen mako a jihar Kano.
Taron na wannan shekarar an yi masa taken “tasirin sanin mutane” ya mayar da hankali ne wajen ƙarfafawa mata gwuiwa wajen iya zamantakewa da ci gaban kansu.
- Babu Uziri A Yaki Da Cin Zarafin Mata – Mohamed M. Fall
- Dokar Haraji: Ƙarawa Masu Kudi Haraji Ba Talakawa Ba Shi Ya Kamata
Haka kuma taron ya samu halartar dubunnan mutane daga sassa daban-daban inda aka koyar da mata dabarun kasuwanci da wayar da kai a kan kula da lafiya, tare kuma da tattaunawa a kan damarmakin da mata suke da su wanda masana suka faɗakar ciki har da Aisha N. Ahmad, tsohuwar mataimakiyar gwamnan babban banki na ƙasa.
Ɗaya daga cikin wadanda suka kafa wannan kungiya, Yasmin Obadaki, ta bayyana cewa taron na bana ɗanba aka kafa saboda suna ci gaba da shirye-shiryen ganin sun karaɗe ko ina a faɗin ƙasar nan domin tallafawa mata su dogara da kansu da kula da lafiya da kuma tallafawa mata na karkara.
Waɗanda suka je taron na bana dai sun ci gajiyar gwajin lafiya kyauta da kyaututtukan da wadanda suka haɗa gwiwa da Mata Network’ suka bayar da dai sauransu.
Yasmin Obadaki ta ce ƙungiyar Mata Network ta shirya tsaf domin cike giɓin da ke tsakanin mata da ingantaccen ilimi da sana’o’i kuma za su ci gaba da nemo hanyoyi domin karfafawa mata gwiwa su tashi tsaye domin taimakawa wajen ci gaban rayuwarsu.