Akwai alamomi masu tayar da hankula daga hedikwatar kasuwancin Nijeriya, wato Legas a daidai lokacin da ake daf da babban zaben 2023, alamomin na tatatre da ‘yancin al’ummar jihar na sauke nauyinsu na kada kuri’a, wanda hakkinsu ne da kundin tsarin mulkin kasa ya basu a matsayinsu na ‘yan Nijeriya na su zabi wanda suke so a zaben da ke tafe.
Alamar iriin wannan barazanar ta auku a shekarar da ta gabata inda wasu matasa suka nemi kona wasu mutum biyu magoya bayan wata jam’iyya saboda suna sanye da rigar da ke alamar jam’iyyar, wannan ya faru ne a garin na Legas. Wasu sojoji dake wucewa ne suka ceci matasan daga shiga cikin wani mummunan hali, amma dai sai da suka karbi dukan da ba za su iya mantawa da shi ba a rayuwarsu.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Kara Goyon Bayan Afirka Ta Tsakiya
- 2023: Abin Da Ya Sa Zaben Tinubu Zai Zama Alheri Ga Nijeriya – C2G-Network
Haka nan kuma makon jiya da jam’iyyar LP ta gudanar da babban taronta na yakin zabe a garin Legas, magoya bayanta sun fuskanci hare-hare da muggan makamai a sassa daban-daban na birnin, inda dama suka ji munanan raunuka da ka iya kaiwa ga rasa rayuka.
Duk da cewa ana iya cewa, irin wannan hare-haren za a iya alakanta sune da ayyuka na ‘yan banga amma yadda lamarin yake faruwa a kai kai kuma a wani yanki na masarautun gargajiya, ya zama dole ya tayar wa da al’umma hankula ya kuma sa a yi matukar damuwa da shi.
A kwanakin baya ne aka ji basaraken yankin Igbara ta karamnar hukuma a Legas, Baale na Igbarra, yana yi wa talakawansa barazanar lallai su zabi wani dan takara ko kuma su fuskanci takunkumi.
A wani jawabi da ya yi na tsawon minti 11 a wani taro a gaban basaraken gargajiyar tare da wasu da ake kyautata zaton jami’an kananan hukumomi ne, an ji suna neman lallai mazauna yankin su kada wa wata jam’iyya kuri’a a jiihar ko kuma su fukanci takunkumi.
Bayanan ya nuna yadda wasu sarakuna gargajiya a yankin Arewacin Nijeriya suke yi wa talakawansu barazanar lallai sai sun zabi wata jami’iyya ko kuma su fuskanci takunkumi, an ruwaito yadda wasu masarautun ke kiran taron gaggawa ana gab da zabe, inda ake tara hakimai da dagatai da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin, a yi musu huduba tare da barazanar lallai sai dai su zabi wata jam’iyya, wadda ake ganin tana da akaka da mahukunta na wannan lokacin. Wadannan ne irin abin yake karfafa ‘yan banga suna kai hari ga masu zabe musamman in sun tabbatar da ba magoya bayan dan takarar su ba ne.
Da farko ina mai yin tir da dukkan hare-haren da ake kai wa ga wasu al’umma da sunan siyasa, ba abin da za a zura ido ba ne ana kallon haka na faruwa. Ko wanne dan Nijeriya yana da hakkin ya bayyana irin ra’ayinsa a kan abubuwan da ya yi Imani dasu da suka shafi addini da siyasa, yana da ikon kasancewa a duk wata kungiyar da yake ra’ayi matukar harkokin kungiyar bai saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya ba kuma bai kamata a tauye masa wannan hakkin ba. Babu wanda ke da ikon hana su wannan hakki nasu. Dole gwamnati ta samar da yanayin da kowa zai sauke nauyn da ke a kansa ba tare da tsoro ba ko barazana.
Idan za a iya tunawa, wannan bashi ne karo na farko da ake samun basaraken gargajiya yana yi wa masu kada kuri’a barazana Jihar Legas ba. A yayin shirye-shiryen babban zaben shekarar 2019, an ruwaito cewa, Sarki a Legas ya yi baraza ga wasu al’umma da suka fito daga wasu sassan Nijeriya barazanar da kada su zabi wata jam’iyya in kuma suka yi haka za su gamu da gamon su, don ya yi barazana zai tura su cikin teku su halaka. Don tabbata da barazanar, ‘yan Nijeriya da suka fito don kada kuri’arsu a wuraren da magoya bayan wannan basaraken suke da yawa sai gashi ana binsu da hare-hare inda aka jikkata mutane da dama, abin takacin a nan shi ne har zuwa yanzu babu wani da aka hukuntra a kan wannan aika-aikar.
A wannan karon, rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta bayar da tabbacin za su gayyaci basaraken don yi masa tambayoyi, wannan matakin zai dakile masu niyyar barazana ga wasu masu kada kuri’a a sassan jihar dama Nijeriya gaba daya, musammmman ganin shi wannan basaraken ya ce, yana aiki ne a bisa umarni, umarnin wa?, dole ya bayyana wadanda suka bashi umarnin tare da kuma bayar da tabbaci al’umma yankin gaba daya na cewa, babu wata barazanar da za su fuskanta a yayin kokarin sauke nauyin su na zabar wa Nijeriya shugaban da zai ja akalar kasar a cikin shekara 4 masu zuwa.
Ya kamata ‘yan sanda a sassan kasar nan su yi koyi da takwarorinsu a Jihar Legas wajen zura ido tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin yi wa wani mai kada kuri’a barazana, ba wai ga masu kada kuri’a kawai ba, ya kamata a tabbatar wa da dukkan ‘yan kasa ‘yancisu na gudanar da dukkan harkokinsu ba tare da tsangwama ba, don akwai rahotannin da ke nuna yadda ake tsangwamar wasu Nijeriya saboda banbancin ra’ayin addini a wasu sassan jihohin arewacin Nijeriya. Saboda haka dole rundunar ‘yan sanda su gudanar da bincike na bai daya don gano yadda ake yi wa wasu al’umma Jihar barazana dama al’umma wasu sassan kasar nan domin kauce wa barkewar tashin hankulla a wuraren da aka san su da zaman lafiya.
Abin lura anan shi ne abubuwan nan da ke faruwa sun ci karo da yarjejeniyar da ‘yan takarar shugabancin kasar nan suka sanya wa hannu a karkashin jagorancin kwamitin Janar Abdulsalami inda suka dauki allkawarin gudanar da harkokin siyasan su a cikin kwanciyar hankali ba tare da yi wa wani ko wata barazana ba, yakamata dukkan jam’iyyun su yi ma magoya bayan su hudubar gudanar da harkokin zabe ba tare da yi wa kowa barazana ba
Daga karshe ina mai tabbatar da cewa, babban ginshikin tsarin dimokradiyya shi ne ‘yanci, ‘yancin zabar wanda dan kasa yake ganin shi zai kai kasar ga tudun muntsira, duk wani nau’i na barazana ko tilasta wa wani ya zabi wani, alami ne da ya sha banban da tsarin dimokradiyya. Da fatan za a yi zabe lafiya.