Rundunar ‘yansandan jihar Legas, ta samu nasarar kama wasu sojojin gona guda hudu.
Asirin sojojin gonar ya tonu ne lokacin da jami’an ‘yansanda da ke Iju karkashin jagorancin DPO Gbenga Stephen suka yi musu dirar ba-zata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Legas SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka ga manema labarai.
An samu nasarar cafke wadannan mutane ne lokacin da ‘yansanda suka tsayar da motarsu kirar Mazda domin yin bincike.
Wadanda aka Kaman su ne Samuel Abel mai kimanin shekara 28 sai Bictor ljeemai mai shekara 35 da Lukman Salabiu mai shekara 43, sai na karshensu Oyinyechi Macus mai shekara 30.
Yanzu haka, an garkame wadannan mutane da ake zargi a ofishin jami’an ‘yansanda masu binciken laifuka da ke Yaba, domin ci gaba da bincikarsu.