Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce, lokaci ya yi da za a duba wasu hanyoyin samun wutar lantarki.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake tofa albarkacin baki kan lalacewar wutar lantarki ta yankin arewacin Nijeriya.
- An Juya Bangare Na Karshe Na Gadar Titi Mafi Tsawo Dake Saman Layin Dogo A Kasar Sin
- Daga Gobe Litinin, Ma’aikatan Jami’a Zasu Fara Yajin Aiki
Lalacewar wutar wacce ta kwashe kwanaki takwas, ta jefa masana’antu asara da gurgunta muhimman abubuwan tattalin arziki a yankin.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce, “Abin takaici ne yadda a yau wasu sassa na Arewacin Nijeriya ke cikin duhu, sakamakon lalata turakun layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Kaduna mai karfin wuta 330kV da ke samar wa jihohin Kano da Kaduna wuta.
An kuma sake lalata layin da ke bai wa Bauchi, Gombe da sauran sassan arewa maso gabas wuta.
“Wannan lamarin na zuwa ne a lokacin da farashin man fetur da dizal a Nijeriya ya azzara, lamarin da ya kara jefa gidaje cikin duhu tare da tilasta rufe wasu masana’antu.
“Wannan ya nuna babban gibin da bangaren samar da wutar lantarkin Nijeriya ke da shi, wannan ya zama dole ne a magance hakan domin kauce wa duk wani cikas a nan gaba.
“Lokaci ya yi da za mu mayar da hankali kan lalubo wasu hanyoyin samar da wutar lantarki don magance bukatunmu na wutar lantarki.”
Kwankwaso ya karfafa gwiwar gwamnatocin jihohi da masu zuba jari masu zaman kansu da su sanya hannun jari a wasu hanyoyin samar da wutar lantarki.