Da sanyin safiyar ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Owerri Babban Birnin Jihar Imo.
Harin ya yi sanadiyyar lalacewar wani bangaren ofishin bayan da nakiya ta fashe.
Kakakin rundunar ‘yansandar Jihar Imo, Mike Abbatam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ya bayyana cewa an samu nasarar kashe maharan guda uku tare da gano bama-bamai guda biyu.
Wannan lamari ya faru ne cikin kwanaki takwas bayan kai farmaki a ofishin INEC da ke karamar hukumar Orlu a cikin jihar.
Wadanda ake zargin ‘yan daba ne sun kai irin wannan farmakin a ofisoshin INEC da ke jihohin Ebonyi da Osun da kuma Ogun a makonni hudun da suka gabata, lamarin da ya fara saka wa mutane shakku kan yuwuwar gudanar da zaben 2023.
Farmakin na Owerri ya gudana ne da misalin karfe uku na dare, inda jami’an tsaro suka samu nasarar harbe uku ciki har da kwamandansu har lahira. An dai samu nasarar kwato bindigogin kirar AK47 da wasu masu sarrafa kansu da motoci takwas daga hannun maharan.
Wata majiya ta ce, “A safiyar Lininin ce wasu ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a ofishin INEC da ke Owerri a Jihar Imo, amma tawagar jami’an tsaro sun samu nasarar bude musu wuta tare da halaka uku ciki har da kwamandarsu.
“An samu nasarar kwato motoci bakwai ciki har da bindigogin AK47 da masu sarrafa kansu. Mafi yawancin ‘yan bindigan sun gudu da raunikan harbi. Amma sai dai ‘yan daban sun kone motar ‘yansanda guda daya.”
Sai dai shi kuma Abbattam ya ce bindigogi kirar AK47 guda uku da motoci aka samu nasarar kwacewa.
Ya ce, “Mun kashe guda uku daga cikin maharan tare da kwato bindigogi kirar AK47 da masu sarrafa kansu muka samu nasarar kwatowa daga hannun maharan. Haka kuma mun kwato abubuwan fashewa guda biyu da motoci uku.”
An dai bayyana cewa an jibge jami’an tsaro a wasu yankuna da ke Owerri sakamakon wannan lamari.
Sakamakon kone-konen ofisoshin INEC a wasu sassan kasar nan, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa (NSA), Majo Janar Babagana Monguno (rtd) da babban sufetan ‘yansanda na kasa, (IGP) Usman Baba Akali sun yi barazanar daukan mataki.
Dukkansu sun karanto laifukan da ke tattare da kone ofisoshin INEC, inda suka bayyana cewa an bai wa jamian tsaro umurnin kalubalantar duk wani mutum ko kungiya da ke kokarin kawo tsaiko kan zaben 2023.
Babban sufetan ‘yansanda ya bayyana cewa tuni ya umurci kwamishinonin ‘yansanda su samar da tsaro a dukkan ofisoshin INEC da ke jihohinsu.
A cewarsa, wannan aiki na wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne da ke barazana ga zaben 2023.
Duk da wadannan zafafan hare-hare da ake kone-konen ofisoshin INEC, hukumar ta bayyana cewa ko kadan wannan ba zai iya hana gudanar da zaben 2023 ba.