Kasar Sin, ta kasance kasa ce mai neman sanya tabbaci da kwanciyar hankali a cikin duniyarmu da ke cike da rudani.
Abin da aka dade ana tsumayi daga cikin kasar Sin da wajenta a fadin duniya, sakamakon cikakken zama na hudu na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) a birnin Beijing, ko me zai haifar?
- Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100
- Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi
Sakamakon zaman da aka fitar kwanan nan, kwamitin tsakiya na JKS ya amince da kafa wasu tsare-tsare da za su zama jagora kan bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 wadanda suka hada da sake tabbatar da shugabancin jam’iyyar baki daya, da sanya kula da mutane a gaba da komai, da neman samun ingantaccen ci gaba, da cikakkiyar zurfafa gyare-gyare a gida, da karfafa cudanya tsakanin kasuwa mai albarka da gwamnati mai kwazon aiki, da kuma tabbatar da samun ci gaba da inganta tsaro.
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa.
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), an kiyasta cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai zarce yuan tiriliyan 35, ko kuma kimanin dala tiriliyan 4.93 na Amurka. In muka dauki matsakaicin ma’aunin tattalin arziki na shekara-shekara na kashi 5.5 cikin 100 daga 2021 zuwa 2024, kasar Sin ta bayar da gudummawar kusan kashi 30 cikin 100 na fadada tattalin arzikin duniya a kowace shekara.
A nan muke cewa, kasar Sin ta jaddada samar da ci gaba da kwanciyar hankali a dangantakarta da kasashen da take makwabta, da kasashen Afirka da ma duniya baki daya.
A farkon wannan watan, shugabar kula da cibiyar asusun bayar da lamuni ta duniya, Kristalina Georgieva ta yi gargadin cewa, ya kamata a yi sulhu a daidaita rikice-rikicen siyasa a gabas ta tsakiya, Gaza da Isra’ila; A Turai, Rasha da Ukraine; Buga Haraji ba misali, wanda duk wannan ke barazana ga tattalin arzikin duniya. Amma duk da ire-iren kalubalen da wadannan cikas din suka haifar, kasar Sin mai tattalin arziki ta biyu mafi girma a duniya ta ci gaba da tafiya a hankali wajen cimma burin ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.
Zaman taron karo na hudu, ya tabbatar da cewa, “akwai sauye-sauye masu sarkakiya da barazana a cikin yanayin da duniyarmu ke ciki a yau, amma tattalin arzikin Sin yana nan da juriya kuma kasar tana kan turbar ci gaba inda akwai damarmaki na habaka tattalin arziki sosai, duk da cewa yanayin rashin tabbas na ci gaba da karuwa”.
Wannan batu ya tabbatar wa al’ummar Sinawa da duniya cewa, masu tsara manufofin Sin sun san kalubalen da ke faruwa a duniya kuma sun shirya tsaf don magance kalubalen.
Sakamakon zaman taron, a fili yake, Sin ta kuduri aniyar ci gaba da saka tabbaci da kwanciyar hankali a duniya. A cikin gida, tsare-tsaren suna nuna sadaukarwa ga inganta karfin kasa da walwalar jama’a. A bangaren sauran kasashe kuwa, suna nanata cewa, kasar a bude take ga masu nufin kulla alaka, tare da haɗa kai, daidaito, da kuma cin gajiyar juna, wanda zai amfani kowa, ba ‘yan tsirarru ba.
Ga kasashe da suka gundura da mulkin danniya suke neman abokan hulda, za su iya dogara da Sin. Ta hanyar kiyaye kwanciyar hankali da tabbatar da zaman aminci a cikin gida da dorewar ci gaba, Sin ta zama kasa mai muhimmanci dake daidaita al’amuran duniya baki daya, wanda hakan na daya daga cikin manyan gudummawar da take bayarwa a yau.














