Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana sanye da kaya na alfarma don shugabantar zaman fada duk da ƙawanyar da jami’an tsaro suka yi wa fadar a yau Jumma’a.
Sarki Sanusi II, tare da sauran ma’aikatan fadar, ya ci gaba da gudanar da zaman fadar cikin natsuwa a fadar. Jami’an ‘Yansanda na Kano ba su bayar da bayanin dalilin ƙawanyar ba, wanda ya ƙara jawo tambayoyi kan lamarin ruɗanin sarauta da ke faruwa a jihar.
- Na Sha Gwagwarmaya Wajen Koyon Ka’idojin Rubutu – Zarah Sunusi
- Kiyaye Rayukan Al’umma: Majalisa Na Shirin Keɓe Wa Masu Sayar Da Iskar Gas Wuri A Wajen Birnin Kano
Haka kuma, babu wani bayani daga majalisar fadar Kano game da taron sarauta da Sarki Sanusi II ya shirya halartar a Bichi.
Rahotanni daga Gidan Gwamnatin jihar sun bayyana cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, yana ƙasar Indiya yin wata ziyara aiki.