Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da bunƙasa duk da matsalolin da ta ke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, ministan ya ce, “Ba za a ce ba a cikin wani yanayi na matsi ba: akwai hauhawar farashi ga kayayyakin masarufin rayuwa da kuma barazana ga halin tsaro a wasu sassa na ƙasar nan.
- Yaƙin Sudan: Gwamnatin Jigawa Ta Samarwa Dalibanta 194 Guraben Karatu A Jami’o’in Cyprus Da indiya
- Gwamna Yusuf Na Neman Amincewar Majalisa Don Kafa Cibiyar Yaƙi Da Cututtuka Ta Kano
“Mu na da cikakkiyar masaniyar haƙƙin kulawa da ya rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya ga kowane ɗan Nijeriya ba tare da la’akari da shekaru, jinsi, addini, ƙabila ko matsayinsa a al’umma ba.
“A ɓangaren tsaro, ana tunkarar duk wata barazana. Mu na kai hari kai-tsaye ga sansanonin ɓarayi, tare da cimma kyawawan nasarori. A makon jiya, an kashe ko an kama ɗimbin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
“Rikicin da ya sake kunno kai a Jihar Filato, a gaskiya abin baƙin ciki ne, amma mu na tabbatarwa kowa da kowa cewa, ana gurfanar da duk masu jawo fitina a sassan ƙasar nan a kotu. Za a yi masu shari’a, kuma za a dawo da zaman lafiya a dukkan wuraren da abin ya shafa.
“Mu na yaba wa namijin ƙoƙarin da hukumomin tsaro da masu farin kaya ke yi, waɗanda ba su yi sanyi a gwiwa ba don tabbatar da cewa mun samu natsuwa a gidajenmu da kan titunanmu, sannan masu aikata laifi ba su samu sauƙi ba.
“Dangane da tattalin arziki, dukkan ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya da abin ya shafa su na aiki tare da juna domin su rage tashin farashi, su daidaita tsarin canjin kuɗin ƙasar waje, kuma su samar da yanayi mai kyau don haɓaka harkar kasuwanci da zuba jari. Irin Nijeriyar da Shugaba Tinubu ya ke ƙoƙarin ginawa ita ce wadda ba a bar kowa a baya ba.
“Ana ta fito da tsare-tsare masu tasiri, waɗanda su ka haɗa da Shirin Bada Rance Ga Ɗalibai, shirin Shugaban Ƙasa na samar da motocin haya na CNG masu aiki da lantarki domin rage dogaro da fetur da man dizel, da sauran tsare-tsaren bada lamuni domin kasuwanci. Shirin samar da motocin zai rage tsadar kuɗin shiga motar haya da sama da kashi 50 cikin ɗari.
“Mu na kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da waɗannan damarmakin da zarar an fito da su, domin an yi su ne saboda kowa ya amfana.
“A daidai lokacin da mu ke tunkarar matsalolin mu haiƙan, ya kamata mu tuna wa dukkan ‘yan Nijeriya da su guji sauraren duk wasu muggan labarai da kalamai na ƙarya da ke jawo rarrabuwar kai. Misali, ba gaskiya ba ne cewar za a mayar da hedikwatar Hukumar Tashoshin Jiragen Sama ta Tarayya ta Nijeriya (FAAN) da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) zuwa Legas saboda dalilai na siyasa domin a ware wani sashe na ƙasar nan. Waɗannan zarge-zargen ba su da wata makama. Maimakon haka, waɗannan matakai ne da su ka shafi gudanarwa domin a inganta harkar aiki da rage kashe kuɗi.
“Ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su kula da duk wasu mutane da ƙungiyoyi a gida da ƙasar waje waɗanda su ka ƙware wajen yaɗa labaran bogi a gidajen rediyo da talabijin da soshiyal midiya, sannan su na yaɗa guntayen bidiyo da hotuna da aka sauya wa fasali don sakawa a intanet.
“A matsayin wani ɓangare na samar da amintaka a tsakanin ‘yan Nijeriya, za a ci gaba da yaƙin nan kan cin hanci da rashawa, kuma za a zurfafa shi. Don tabbatar da cewa babu wani ɗan lele, kuma an yi amfani da dukiyar jama’a wajen yi wa jama’a aiki, Shugaba Tinubu ya na sama wa hukumomin yaƙi da cin hanci dukkan goyon bayan da su ke buƙata domin gudanar da aikin su.
“Ba za mu cimma nasarar gina irin Nijeriyar da mu ke so ba idan har mu ka kafe kan kallon ƙalubalenmu da matsalolinmu kaɗai, ba ɗimbin damarmaki da kyawawan labarai da ke zagaye da mu ba. A sane mu ke cewa ƙasar na ci gaba da samun burin zuba jari daga ‘yan kasuwa na gida da na waje.
“Kada mu manta da ainihin abin da yake dahir: wato maimakon rarrabuwar kai da gaba da juna, za mu iya zama tare kuma mu bunƙasa cikin haɗin kai da fata tagari, tare da tabbacin cewa duk da waɗannan matsalolin masu wucewa da koma-baya da ake samu daga lokaci zuwa lokaci, babbar nasara ta na gab da zuwa.”