Wata kwararriya a fanin kiwon Zuma a kasar nan Uwargida Obianuju ta ce, kiwon na Zuma ana samun ribar dala biliyan 450 a duniya.
Ta bayyana hakan a jawabinta a wajen taron masu ruwa da tsakai a fannin, inda ta kara da cewa, wannan adadin kudin da ake samu a matsayin riba, ya kai kimanin naira tiriliyan 162, inda kuma albarkar da ake samu ta kai kimanin dala biliyan 250 daidai da naira tiriliyan 90.
Obianuju ta ci gaba da cewar, sarrafa Zumar a fadin duniya ta kai yawan tan miliyan 1.8, inda ta kai dala biliyan 11.5 kimanin naira tiriliyan 4.14.
A bisa yadda girman kasuwar take a Afirka wadda keda Zumar mai inganci tanada kashi biyar a cikin dari an kuma kiyasta ta kai tan 90,000, a saboda haka kwararru suke ganin akwai bukatar daukar matakai don gyara hakan.
Ta ce, Nijeriya ce kusam akan gaba nahiyar Afirka wajen kiwon Zuma, inda take samar da Zuma tan 40,000 da aka kiyasta kudin ya kai dala miliyan 255.3 kimanin naira biliyan 91.9.
A cewarta, Nijeriya, tana samar da Zumar data kai tan 15,000 da aka kiyasta ta kai dala miliyan 96.02 daidai da naira biliyan 34.6.
Ta bayyana cewa, ga manomin da yake son zuba jarinsa a fannin, yana bukatar naira 210,000 ,wajen kiwon guda goma, da Zuma hadada da cakin yin kiwon, safunan hannu biyu, takalma biyu, karfen zungoro Zumar da kuma tukunyar yin hayaki daya.
“A bisa zuba wannan jarin, manomi zai iya samun Zumar data kai yawan kilogiram 150 da wajen kiwon da ya kai kilogiram 37, inda zai iya samun kimanin naira 524,000 a kiwo daya ko samada haka mafi yawanci bayan watanni shida.”
Shi ma wani kwararre a fannin Oluwaseun Johnson, ya bayyana cewar, kashi biyu bisa dari na kiwon Zuma a duniya na Zumar da
Kiwon Zuma fanni ne dake tattare da alfanu wajen ciyar da tattalin arziki, saidai mafi yawancin manoma matasa suna gujewa fannin duk da alfanun da fannin take dashi.
Masana a fannin, sunyi amanar cewar fannin yana tartare da dimbin alfanun da zai iya samar da sauyi yadda manoman za su iya kara samarwa da kansu kudin Shiga in bar suka rungumi fannin.
Wata kwarararriya a fannin Obianuju Okpo, ya danganta fannin a matsayin hanyar da ko a fadin duniya ake samun kudi a cikin yan watanni, inda ya kara da ce fannin kuma yana habaka tattalin arzikin kasa matuka.
Ta kai ta iri ana samun 3000, in an samu waje mai kyau.
Daga dala biliyan 235 zuwa dala biliyan 577 na abincin da ake sarrafa wa a duniya, ya danganta ne akan yadda masu sarrafa ta suka kware, sai dai, a ba’a san takamaiman arzikin da ake samu a fannin ba a fadin duniya tana kuma samar da kashi 90 bisa dari.
Ita ma Shugabar sashin sarrafa kaya da ke Cibiyar fitar da kaya kasar waje NEPC Uwargida Ngozi Ibe ta ce, bukatar kayan kiwon na Zuma yana kara-karuwa gannin yadda masna’antu suke kara bukatar su don yin kiwon da zasu kai har kasar waje.
Ta buga misali da cewar, daya daga cikin kayan aikin da ake kira a turance (beeswad), da ake yin amfani dashi a cikin man shafawa da saurasu farashin sa a kasuwar duniya ya kai dala 10, inda ta ce, sauran kayan sun hadada, wanda ake kira a turance ( bee Propolis) da ake yin amfani dashi wajen wankin hakora da kiwon lafiya da man shafawa.
A cewar ta, sanadarin Zuma da a turance ake kira(benom) wanda kuma ake yin amfani dashi wajen yakar Kansa da ciwon kashi ana sayar dashi akan dala 2,000 na dukkan giram daya.
A karshe kwararrun sukace, manomi baya bukatar wata gona don ya fara kiwon, inda kuma suka baiwa manoman shawarar dasu rungumi sana’ar.