• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

by Rabi'at Sidi Bala
1 month ago
Wanda

Wannan ci gaban hirar da wakiliyarmu Rabi’at Sidi Bala ta yi da jaruma a masana’antar Kannywood Hauwa Garba wadda aka fi sani da Sabuwa. A yi karatu lafiya

Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka, wanda ba za ki taba mantawa da shi ba, game da fim?

  • Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
  • Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

Gaskiya ne, ba zan taba mantawa da jama’ar da Allah ya ba ni ba, kuma a harkar ce. Da ban shiga Kannywood ba kila ba za a sanni ba, amman na shigo Kannywood da taimakon Allah, kuma gashi Allah ya sa kowa ya sanni, ba inda zan shiga ba a ce wance ba. Kuma duk wani abu da za a ci, a sha, a saka a baki, wallahi bai gagare ni ba, Allah ya rufa min asiri. To, ko wannan ma ai abun farinciki ne da jin dadi.

 

Ya ki ka dauki fim a wajenki?

LABARAI MASU NASABA

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma nake zaune cikinsa.

 

Ko kina da ubangida, a cikin masana’antar Kannywood?

Ai ni a masana’antar duk wani sa’a na, ko wanda ya girmen ubangidana ne, ni ba butulu ba ce da zan ce ban da iyayen gida.

 

Ana rade-radin akwai yaranki a cikin masana’antar Kannywood, mene ne gaskiyar maganar?

‘Ya ta guda daya ce take Kannywood, saboda da kanta ta ce “Umma ina so na rika irin sana’ar ku” na ce mata to. Na sa ta tambayi babanta, ‘yan’uwana duk aka tattarasu aka yi musu maganar, suka ce ba komai ni ma ai ina yi. Ta ce “Umma fita za ki yi?” na ce, ba zan fita ba kowa ya yi, ai masana’anta ce me hada da da uwa da uba da kaka da jikoki, da tattaba kunne ce. Na ce ta je Allah ya sa albarka, a lamarin kuma na barta tana yi. Sunanta Maryam Intike.

 

Bayan sana’ar fim, kina wata sana’ar ne?

Eh, ina sana’a. Amma sana’a ta, idan na tashi zan je kudu sarin kaya, ina saro kaya a kudu kamar; Takalma, Sarka da ‘Yan’kunne, irin su Jigida na mata, duk ina saro su. Sannan in zan tafi kuma daga nan, ina tafiya da; Magarya, Kurna, Taura, Tsamiyar Biri, Aduwa, Iloka, Tuwon Madara, Goruba garinta da guda-gudar ta da bararriya mara kwallo. Duk ina kukkulla su ina tafiya da su, da Turaren Humra, Kwalakca, da turaren wuta, ina tafiya da soyayyiyar Fara me rai da lafiya, da Dambun Nama. Duk ina zuwa da su Kudu, idan na gama siyar da su, sai na siyo wadannan kayan sai na dawo. Amma a shekara, sau daya nake zuwa. Sannan ina siyar da Shadda, Atampa, Gyale, amma gaskiya su Katsina nake kai su wajen ‘yar’uwa ta ita take siyar min, sai karshen wata ta turo kudin, sai a kara siya a tura. Nan ma idan mutum na so ya tura min, zan bayar, ina siyar da Huluna irin na maiduguri, amma su kwannan nan na fara.

 

Shin kin taba fuskantar wani kalubale daga wajen masu kallo, musamman wajen fita unguwa ko kasuwa ko makamancin hakan?

Masu kallon nan indai ba farin sani suka yi min ba to, ba za su taba iya gane ni ba. Ni ba a gane ni, in har aka ga an gane ni daman mutum yana mu’amula da ni. Shi ya sa nake shiga cikin kasuwa na yi duk abin da zan yi na dawo ba ruwa na. Ba wanda zai ce ‘Yar’auta, ban taba saka nikab na shiga kasuwa ba, fuskata ‘free’ nake shiga Kasuwa. Ko’ina kuma ina zuwa in har na ga an gane ni to, zan sauri na bar wajen kar a tara min jama’a. Kin san in aka tara maka mutane sai a zo a yi abin da ba daidai ba, ba wai muna gudun jama’a ba, dole ka so jama’a dan su ka ke yi. Amma wani lokacin sai a tara maka jama’a ga wane-ga wane wani can da gudu zai rugo ya zo ya yi maka illa ana tunanin so ne, nan kuma ga wani can baragurbi ya shigo.

 

A misali ki zama shugaba cikin masana’antar Kannywood, wane irin gyara ko cigaba za ki kawo a masana’antar Kannywood?

Idan na zama shugaba a Kannywood me fada a ji, wallahi duk ranar Alhamis da Juma’a in sha Allahu sai na saka malamai ai ta yi mana addu’a, duk abin da yake ba na daidai ba Allah ya fidda mana a cikin Kannywood. Abin da yake na daidai Allah ya kara daukaka shi ya darajanta shi, ya kara mana albarka a cikinsa. Tunda akwai abin da ake baka san da shi ba, kana shugaba ba komai za ka sani ba. Kawai addu’a ita ce gaba, ka zama kai kullum me addu’a ne kamar yadda ka ke a gidanka.

 

Wane sako ki ke da shi ga masoyanki, masu kallon finafinanki?

Abin da zan ce da masoyana, yadda ku ke so na, ku ke kallon finafinau na Allah ya saka muku da alkhairi, kuma ina godiya Allah ya raya muku zuri’a. Sauran yara Allah ya basu ilimi na addinin musulunci.

 

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga cikin masana’antar Kannywood?

Shawarar da zan ba su mazansu da matansu, na farko dai su rike salloli, su rika addini cikin lokaci. Sun ga yadda ake farfadar magana a kanmu, dan Allah ku rika addini kuna rokon Allah, Allah zai kubutar da mu da ku akan makiya. Sannan kuma ku zauna lafiya da iyayenku, idan iyayenku na da rai ku yi ta kyautata musu, Allah zai kyautata muku. Sannan ku zama masu ladabi da biyayya a cikin masana’antar, in aka ce ka yi to, ka yi, in aka ce ka bari to, ka bari. Sannan kuma duk wani baragurbi na cikin masana’antar komai girmansa, in mata ne ya neme ku da wata maganar banza, ku je ku kai wa manyan mu za su dauki mataki da iznin Allah.

 

Ko kina da wata shawara da za ki bawa, sauran abokan aikinki dake masana’antar Kannywood?

Kiran da zan yi ga abokan sana’a ta, manyanmu ni dai zan kira, ya kamata a tattara mu bakidaya, a zauna a yi babban ‘meeting’ na kowa da kowa manya da yara. A nuna mana dan’uwan mu idan ya fito ba shi da lafiya, mu ya kamata mu taimake shi, ba a je can a yi ta talla, a je nan ba. Mu tsaya mu hada kai mu taimake shi idan ba shi da lafiya. To, wallahi akwai mutum biyu ban da lafiya ko yanzu watana biyu ban da lafiya, wallahi tallahi akwai wani aiki da muke yi me suna ‘SO NE’ na Sultan. Sai na ga ai yana da kirki ban taba aiki da shi ba sai wannan, ina asibiti ba ni da kudi ga kudi sun kare, ga allurori ba kudi, aka ce a cikin ‘yan fim din mu wa zan kira? na duba lambar mutum biyu na gani, da ta Sultan da ta Daushe. Na kira Daushe na ce “Daushe kai wa girman Allah ka taimaka min, ba ni da lafiya ko wani abu ne ka bayar, gashi kudi sun kare min muna asibiti” ya ce na bari yana mota idan ya sauka zai kira ni. Wannan maganar da nake wata biyu kenan har yau bai kira ni ba. Sultan na kira shi, na fada masa ba ni da llafiya ina asibiti, ya ce Asibiti lafiya? na ce ban da kudi, kudin mu sun kare wajen dubu arba’in mun siyi magunguna da ake yi min karin ruwa da allurai. Sai ya ce min to! nawa ne sauran? ya ce na tambaye su, aka rubuto magnguna wajen likita, aka rubuta magani dubu dari da ashirin da biyar. Da na tashi na kira Sultan na fada masa kudin, ya ce sun yi yawa, na ce, za ka iya bayar da ko ya ya ne, wani ma sai ya bayar a haka har a hada, sai ya ce turon lambar bankinki na tura masa. Aka wuni bai turo ba, aka kwana bai turo ba, akai ta wuni ana kaiwa dare. Sai na ce maman mu bari na kara kiransa, sai ta ce to, sai na kira shi. Ina kiransa ya daga ya ce min a’a Auta, ina zuwa yanzu-yanzun nan da daddaren nan za ki ga abin da zan turo miki. Na ce, to! na gode, Allah ya saka da alkhairi. Kin ga har yau bai kara yi min magana ba to, ta ina za a ce muna taimakon junan mu. A dawo daidai manyan mu a rika taimakawa juna, a daina sa mu a media kowa yana jin maganar mu in dan Allah ne.

Muna godiya, ki huta lafiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Next Post
Sin Da AU Sun Yi Alkawarin Daukaka Tsaro Da Adalci A Duniya

Sin Da AU Sun Yi Alkawarin Daukaka Tsaro Da Adalci A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.