Jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da shugaban majalisar shugabannin kasashen Turai Charles Michel a nan birnin Beijing. Yayin tattaunawarsu, Xi ya gabatar da shawarwari guda 4 game da bunkasuwar huldar bangarorin biyu. Xi yana fatan EU za ta zama muhimmiyar abokiyar Sin yayin da take kokarin zamanintar da kasar, bisa salonta.
A nasa bangare, Charles Michel ya nuna cewa, EU na fatan zama sahihiyar abokiyar kasar Sin, wajen goyon bayanta a cikin dogon lokaci. Tattaunawarsu ta nuna aniyyar kara hadin kan bangarori biyu don samun bunkasa tare.
A baya, wasu mambobin EU na kuskure game da batun kasar Sin. Abin da ya illata dangantakar bangarorin biyu, har ya lahanta muradun Turai.
A yayin ganawarsu, Charles Michel ya yi imanin cewa, EU za ta nace ga manufar kasar Sin daya tak a duniya, da mutunta ikon mulki da cikakkun yankunan kasar Sin, ba kuma za su tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ba. Kazalika, yana fatan bangarorin biyu, za su kara tuntubar juna kai tsaye da inganta mu’ammala da hadin kansu. Ba shakka nagartaciyyar huldar bangarorin biyu, za ta ba da gudunmawa wajen samar da tushen siyasa mai karko a tsakaninsu.
A matsayinsu na manyan kasuwannin duniya, Sin da Turai na da nauyin dake wuyansu na tabbatar da ganin, an tafiyar da harkokin duniya tsakanin bangarori daban-daban, da kiyaye zaman lafiya da bunkasuwar duniya tare.
Saboda ganin cewa, yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki a halin yanzu, hadin kan bangarorin biyu na da muhimmanci matuka. Sin na fatan Turai za ta nace ga tsai da manufofinsu bisa radin kansu, da ingiza dangantakar abota tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa gaba, ta yadda za su kawowa juna dammamaki, wanda zai aza tubali ga samun kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Amina Xu)