Yanzu haka, duniyarmu na fuskantar manyan sauye-sauyen da ba’a taba ganin irinsa ba. Kasancewarsu manyan kasashe biyu, yadda Sin da Amurka suke hulda da juna, na haifar da muhimmin tasiri ga makomar dan Adam da ta duniya. Kamar dai yadda mataimakin babban editan jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ya fada, “Sin da Amurka kasashe biyu ne mafiya tasiri a duniya, wadanda suke daukar babban nauyi na kiyaye kwanciyar hankali da ci gaba a duniya.”
To ko ina ne huldar kasashen biyu za ta dosa? Akwai zabi guda biyu a gabansu, na farko shi ne daya ta dage neman nasara daga faduwar dayar, ta rura wutar adawa tsakanin sassa daban daban, kana ta jagoranci duniya zuwa turbar yamutsi da rarrabuwar kawuna; Na biyu kuma shi ne karfafa dunkulewa, da hadin gwiwa da aiki tare, don warware kalubalen da duniya ke fuskanta, da ingiza nasarar tsaro da wadata a duniya. Wadannan zabi 2 na wakiltar alkibla biyu mabambanta, wadanda za su haifar da sakamako biyu masu bambanci da juna.
- Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Kasar Amurka Domin Gudanar Da Taron Shugabannin Kasashen Sin Da Amurka Da Taron APEC Karo Na 30
- Ganawar San Francisco: Tsaraba Daga Jawabin Shugaba Xi Kan Bukatar Sin Da Amurka Su Nuna Su Manya Ne A Aikace
Hakika, ganawar shugabannin kasashen biyu a ranar 15 ga wata a birnin San Francisco na kasar Amurka, ta samar da amsa game da me ya kamata kasashen biyu suka zaba, wato ya kamata kasashen Sin da Amurka su yi sabon hangen nesa, tare da gina ginshikai biyar tare, don inganta alakar dake tsakaninsu. Na farko, habaka daidaitacciyar fahimta tare, Na biyu, magance rashin jituwa tare yadda ya kamata. Na uku, ciyar da hadin gwiwar moriyar juna gaba tare, sai na hudu, sauke nauyin dake wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe. Kana na biyar kuma na karshe, shi ne inganta mu’amala tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Wannan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai San Francisco ta kasance ziyarar da ya kai kasar ta Amurka bayan tsawon shekaru shida, haka kuma ganawar da ya yi tare takwaransa na Amurka Joe Biden, ta wakana ne biyo bayan ganawar da suka yi a tsibirin Bali na kasar Indonesia a shekarar bara. A yayin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, “takara tsakanin manyan kasashe masu karfin fada a ji ba ita ce taken wannan zamani ba, kuma ba za ta warware matsalolin Sin da na Amurka da na duniya baki daya ba. Wannan duniya na da fadin da zai wadatar da Sin da Amurka, kuma nasarorinmu damammaki ne gare mu baki daya.”
A hakika, dalilin da ya sa huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta shiga mawuyacin yanayi a shekarun baya shi ne, yadda Amurka ta yi kuskuren daukar Sin din a matsayin babbar abokiyar takara da ta fi yi mata barazana, abin da ya sa ta dauki munanan matakan da ba su dace ba.
Yadda huldar Sin da Amurka za ta bunkasa a hakika ta dogara ne ga yadda kasashen biyu suke fahimtar juna. In dai suna daukar juna a matsayin abokan hadin gwiwa, to, huldarsu za ta yi ta inganta. Amma idan sun dauki juna a matsayin abokan takara, to, za a kara samun yanayi na fito na fito a tsakaninsu.
Ba ma kawai Sin da Amurka za su amfana daga kyakkyawar huldar da ke tsakaninsu ba, har ma da kasashen duniya baki daya. Kamar yadda masanin kasar Senegal kan nazarin harkokin kasar Sin Amadou Diop ya fada, duniya da ke neman karin hadin kai, da bude kofa ga juna, da ma albarka na bukatar a maido da huldar Sin da Amurka kan turbar da ta kamata. “Sin da Amurka dukkansu manyan abokan ciniki ne ga Afirka. Kyakkyawar dangantakar kasashen biyu na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da bunkasar tattalin arziki, da ciniki, da zaman lafiya, da tsaro, da dauwamammen ci gaba a Afirka. Don haka, Afirka na bukatar Sin da Amurka su kara inganta huldarsu.”
A yayin ganawarsu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi a yi la’akari, gami da tsara shirin raya dangantakar Sin da Amurka, ta yin la’akari da makomar dan Adam da ta duniya.
Daga tsibirin Bali har zuwa San Francisco, farfadowar huldar Sin da Amurka ba abu ne mai sauki ba, abubuwan da suka faru sun shaida cewa, muddin dai an tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma, za a kai ga kyautata huldar kasashen biyu, kuma duniya na fatan a tabbatar da daidaiton da aka cimma a San Francisco. (Lubabatu Lei)