A yayin da jama’a a sassa daban-daban na duniya ke murnar shiga sabuwar shekara ta 2024, su ma shugabannin kasashen Sin da Amurka sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A cikin sakonsa, shugaban kasar Sin Xi ya ce, kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, wani babban al’amari ne a tarihin alakar dake tsakanin kasashen biyu da ma na kasa da kasa.
- Harbin Kasar Sin Ya Samu Bunkasuwar Yawon Shakatawa A Lokacin Hutun Murnar Sabuwar Shekara
- Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Sin Game Da Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Amurka
Sanin kowa ne cewa, a cikin shekaru 45 da suka gabata, alakar kasashen biyu ta fuskanci wasu ’yan matsaloli, saboda nuna fuska biyu da bangaren Amurka ke yi, da yadda a wasu lokuta yake rashin cika alkawarun da ya dauka kan hadin gwiwar kasashen biyu, ko tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa ko dai da batun tsaro ko demokuradiya ko kakkabawa kamfanoni da ma daidaikun Sinawa takunkumai na kashin kai, wadanda a mafi yawan lokuta sun sabawa dokoki da yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da ma na kasa da kasa, amma dai baki daya ana iya cewa, alakar ta ci gaba, wanda ba wai kawai ta kyautata jin dadin jama’ar kasashen biyu ba, har ma ta inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duk duniya.
Tarihi ya riga ya tabbatar kuma zai ci gaba da tabbatar da cewa, mutunta juna, zaman lafiya da hadin gwiwa da samun moriyar juna, ita ce hanyar da ta dace kasashen Sin da Amurka su daidaita da juna, a matsayinsu na manyan kasashe biyu. Kuma ya kamata ta zama alkiblar kokarin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a sabon zamani.
Kasar Sin ta sha bayyanawa cewa, a shirye take ta yi aiki tare da bangaren Amurka, don ci gaba da tafiyar da dangantakar kasashen biyu, ta yadda hakan zai amfanar da kasashen biyu da jama’arsu, da kuma sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. Don haka, ya dace bangaren na Amurka ya rika aiwatar da abubuwan da ya fada a zahiri ba wai maganar fatar baki ba. Mu gani a kasa, wai ana biki a gidansu kare.
A cikin tasa wasikar taya murna, shugaba Biden ya ce, tun lokacin da aka kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1979, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin, ta samar da wadata da damammaki a kasashen Amurka, da Sin da ma duniya baki daya.
A wannan karon ya ce, yana fatan dorawa kan ci gaba da magabatansa suka samu, da dimbin tarurruka da tattaunawar da ya yi da shugaba Xi, don ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. Fatanmu dai shi ne, jagororin Amurka, za su rika aiwatar da dukkan abubuwan da suka fada a zahiri. A fada a cika, shi ne dattaku. Yanzu dai mun yi ban-kwana da shekarar 2023, muna fatan kasashen duniya za su rika kyautata alakar dake tsakaninsu a asabuwar shekarar 2024, ta yadda za mu gina duniya mai zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata, wadda kowa da kowa zai ji dadin zama a cikinta. (Ibrahim Yaya)