A ranar 1 ga watan Agustan nan ne, ake bikin cikar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin shekaru 95 da kafuwa.
Rundunar sojojin kasar Sin, wadda aka kafa daga birbishin yaki, ta san cewa zaman lafiya ba abu ne mai saukin samu ba, don haka ta dauki aikin tabbatar da shi a matsayin manufar ta.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, rundunar ta kara kaimi matuka ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya.
Ta ci gaba da tura dakarun rundunar ruwa har 41, masu aikin rakiyar jiragen ruwa a mashigin tekun Aden, da tekun gabar Somalia, inda suka yi rakiyar sama da manyan jiragen dakon kaya na Sin da na sauran kasashen duniya 7,000.
Kaza lika, jirgin ruwan aikin jinya na tafi-da-gidan ka na rundunar ko “Peace Ark” a Turance, ya ziyarci kasashe 43, inda ya ba da jiyya ga sama da mutane 230,000 a sassan kasashe da yankuna masu yawa.
Rundunar sojojin kasar Sin ta ci gaba da samar da tallafin tsaron lafiya ga sassan al’ummun kasa da kasa, karkashin manufar samar da al’ummar bai daya, mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil adama ta hanyar gudanar da ayyuka na zahiri. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)