Da tsakar ranar Laraba 30 ga watan Nuwanban shekarar 2022 ne, kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), da zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalissar gudanarwar kasar, da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, da hukumar kolin rundunar sojoji ta JKS da jamhuriyar jama’ar kasar Sin suka tabbatar da rasuwar tsohon babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin.
A yayin cikakken zama karo na 4 na kwamitin kolin JKS na 13 da aka gudanar a watan Yunin shekarar 1989, an zabe shi a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS. Ya rike wannan matsayi, daga watan Yunin shekarar 1989 zuwa watan Nuwamban shekarar 2002.
Sannan a yayin babban taron jama’ar kasar Sin karo na 8 da aka gudanar a watan Maris na shekarar 1993, an zabe shi a matsayin shugaban kasar Sin. Ya zama shugaban kasar Sin a tsakanin watan Maris na shekarar 1993 zuwa watan Maris na shekarar 2003.
A lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasar Sin, marigayi Jiang Zemin ya kai ziyarar aiki tarayyar Nijeriya a watan Afrilun shekarar 2002, domin kokarin bunkasa dangantaka da kuma sada zumunta tsakanin kasar Sin da Nijeriya.
An bayyana Jiang Zemin a matsayin jajirtaccen shugaba mai martaba, wanda dukkanin ’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin suka aminta da shi, wanda ya samu karbuwa daga rundunar sojojin kasar Sin, da daukacin al’ummar Sinawa, kana babban mabiyin akidar Markisanci, kuma babban masani a fannin siyasa da ayyukan soji da diflomasiyya, jarumin jam’iyyar kwaminis da ya taka rawar gani, kuma shugaba na-gari a tafarkin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. Kaza lika marigayin jigo ne na jagororin kasar Sin na zuriya ta uku, wanda ya kafa ginshikin ka’idar mulki ta “wakilci a fannoni uku.
Tun lokacin har zuwa yanzu, shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama, suka aike da wasikun ta’aziya ga shugaban kasar Xi Jinping, inda suka nuna jimami game da rasuwar Jiang Zemin, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sinawa da kyautata matsayinta a duniya, inganta dangantakar dake tsakanin Sin da kasashe daban-daban, kuma dan siyasa mai kima da fara’a, jagoran da ya tsaya tsayin daka domin ganin kasar Sin ta shiga cikin harkokin kasa da kasa, da shigar da kasar cikin kungiyar cinikayyar duniya, kana gwarzo da ya jagoranci Sin wajen karbar bakuncin babban taron mata na duniya karo na hudu dake da babbar ma’ana.
Sun kuma amince cewa, tsakanin karshen shekarun 1980 da farkon shekarun 1990, lokaci ne mai matukar muhimmanci ga makomar jam’iyyar ta kasar ta Sin, a lokacin marigayi Jiang Zemin ya jagoranci shugabannin kasar wajen cimma sabon ci gaba na aiwatar da sauye-sauye, da bude kofa a Sin, da ma zamanintar da kasar mai mulkin gurguzu.
Hakaki an yi rashin gwarzo, wanda duniya ta shaida gagarumin rawar da ya taka a lokuta daban-daban, wadanda suka kasance masu muhimmanci ba kawai ga kasar Sin ba, har ga duniya baki daya. Halin mutum aka ce jarinsa. Mariyagi Jiang Zemin ya mutu ne, yana da shekaru 96 a duniya. Ya kuma bar kyawawan halaye abin koyi. (Ibrahim Yaya)