Shugabannin Duniya na ci gaba da zaman makoki na mutane sama da 3,000 da suka mutu sakamakon girzizar kasa da ta auku a Turkiyya da kuma a Arewa Maso Gabashin Siriya.
Iftila’in ya kuma janyo dubban mutane da suka samu raunuka tare da raba su da mahuallansu, inda kuma ake ta kokarin kubutar da sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su.
- An Gurfanar Da ‘Yan Bangar Siyasa 10 A Gaban Kotu A Sakkwato
- NIS Ta Kwato Katin Zabe 106 Daga Hannun Bakin Haure A Kwara
Nauyin girgizar ya kai 7.8, inda kuma iftila’in ya kara haifar da matsala musamman ga miliyoyin ‘yan Siriya da ta shafe shekaru ta na fama da yaki.
Wani dan kasar Siriya Abdul Salam al-Mahmou, ya bayyana cewa, girgizar ta zo ne kamar tashin duniya, inda ya kara da cewa, ta taho ne sanyi sai kuma ruwan sama, akwai kuma bukatar a kubutar da rayuwar jama’a.
Sashen kula da binciken yanayi na Kasar Amurka ya ce, girgizar ta kasance mafi girma da aka taba samu a fadin duniya tun bayan wacce ta auku kudancin Atlantik.
Ministan Lafiya na Turkiyya, Fahrettin Koca, ya sanar da cewa, yawan wadanda suka rasu a Turkiyya ya kai 1,651, inda kuma mutane 11,119 suka samu raunuka.
Bisa adadin da gwamnatin kasar Siriya ta fitar ta ce, akalla mutane 1,073 suka rasu.
Adadin wadanda suka samu raunuka a jiya litinin ya haura na girgizar kasar da aka yi a Turkiyya a 1999 shine mafi yawa.
Shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdogan, wanda ya ke tunkrar zabe mai zafi a watan mayu mai zuwa, ya danganta iftila’in a matsayin mafi muni akan wacce ta auku a 1939.
Har ila yau, Siriya da ta fuskanci yakin basasa da aka shafe shekaru 11 ana yi, ministan lafiya na kasar ya ce, an kashe mutane 593, inda kuma mutane 1,326 suka samu raunuka.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya nuna kaduwarsa akan iftila’in da ya auku a kasashen biyu, inda kuma ya yi alkawarin taimaka wa kasashen biyu.
Fafaroma na Vatican Pope Francis shi ma ya nuna alhininsa akan iftila’in da ya aukawa kasashen biyu.
Bugu da kari, gwamnatin Birtaniya ta ce za ta masu yin ceto da tawagar likitoci zuwa kasar Turkiyya.
Shi ma a na sa sakon na jajanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyar sa ga kasashen biyu.