• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duniyarmu Na Da Girman Da Ya Ishi Kasa Da Kasa Su Samu Ci Gaba Tare

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Duniyarmu Na Da Girman Da Ya Ishi Kasa Da Kasa Su Samu Ci Gaba Tare
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Akwai wata kasar da ta kafa sansanonin soja kimanin 750 a ketare, wadanda suka barbazu a kasashe da shiyyoyi 80 na Asiya da Turai da gabas ta tsakiya da Afirka da Latin Amurka, matakin da ya sa ta zama kasar da ta fi yawan mallakar sansanonin soja a duniya. To, haka ne, ita ce Amurka.

Duk da haka, kasar ta Amurka ta yi ta yada jita-jita cewa wai “akwai barazana daga tashoshin jiragen ruwa da kasar Sin ta zuba jarin gina su a fadin duniya”, wadda ta shelanta cewa wai “tashoshin na iya samar da tallafi ga sojojin ruwan kasar Sin”. Wani abokina dan Nijeriya ya tambaye ni ra’ayina kan batun bayan da ya karanta rahoton.

  • Kasar Sin Na Goyon Bayan Shimfida Zaman Lafiya A Colombia

Lallai furucin ya ba ni dariya, mun sha jin “tarkon bashi” da “sabon salon mulkin mallaka” daga bakinsu a baya… ga shi yanzu har an alakanta tashoshin ruwa wajen shafa wa kasar Sin bakin fenti. Gaskiya sun yi iyakacin kokari wajen dakile kasar Sin.

Sinawa kan ce, ba a damuwa da rashin dalili idan ana son dora laifi kan wani, kuma wannan magana ta dace ayi amfani da ita a kan kasar Amurka, domin kuwa, Amurka ba ta taba mai da hankali a kan abubuwan da kasar Sin ta yi, a maimakon haka, kullum hankalinta na kan ta yaya za ta gano abin da zai shafa wa kasar Sin kashin kaza.

Sanin kowa ne sufurin teku ya kasance hanyar sufuri mafi muhimmanci a hada-hadar cinikin duniya, don haka ma, tashoshin jiragen ruwa na taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasa. Bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, kamfanonin kasar Sin sun yi ta kokarin sa hannu cikin ayyukan gina tashoshin jiragen ruwa a kasashen da suka amince da shawarar, matakin da ya yi matukar inganta samar da guraben aikin yi da ababen more rayuwa da kuma tattalin arzikin kasashen.

Labarai Masu Nasaba

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Misali a Nijeriya, tashar jiragen ruwa ta Lekki da kamfanin kasar Sin ya sa hannun zuba jari da ma gina ta, ta kasance tasha mai zurfin ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, haka kuma daya ne daga cikin jiragen ruwa mafi girma a shiyyar yammacin Afirka. Tun bayan da aka fara aiki da ita a farkon wannan shekara, tashar ta taimaka wajen fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa ketare, musamman ma amfanin gona, an kuma yi hasashen tashar za ta samar da guraben aikin yi kimanin dubu 200 nan da shekaru masu zuwa, wadda za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ga shi irin wadannan tashoshin sun zamanto barazana a bakin kasar Amurka. A hakika, da yardar kasashen ne kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kuma ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu ba, balle ma a ce ta haifar da barazana ga tsaron wata kasa. Bisa kididdigar da bankin duniya ya yi, daga shekarar 2015 zuwa ta 2030, kimanin mutane miliyan 40 ne za su fita daga kangin talauci sakamakon hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya.

Don haka ma, akasarin kasashe sun nuna yabo ga hadin gwiwar da suke yi da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya, akasin yadda Amurka da wasu kasashen yamma suka nuna “damuwa”. Dalilin hakan kuma shi ne hadin gwiwar ya karfafa mu’amalar tattalin arziki da al’adu a tsakanin kasashen, tare da kara karfinsu a duniya, matakin da kuma ya ba Amurka matukar damuwa, sakamakon yadda hakan ya zama barazana ga babakeren da ta kafa a duniya. Don haka, sai aka ga Amurka ta na ta kokarin yada jita jita a duniya, a kokarin bata sunan kasar Sin da ma hadin gwiwarta da kasashen duniya.

Sinawa kuma kan ce, “Sai wanda ya sa takalma ne zai san ko ya dace”. Kasashen da suke yin hadin gwiwa da kasar Sin suna da hikima da kuma kwarewa wajen tabbatar da ko hadin gwiwa ya dace ko a’a, kuma ba su bukatar “malami” ya yi musu lacca.

Duk ci gaban da za ta samu, ba za ta kafa babakere ko fadada ikonta a duniya ba, wannan alkawari ne da kasar Sin ta dauka. Amma Amurka a nata bangare, me ya sa ta kafa tarin sansanonin soja a sauran kasashen duniya?

Daga karshe, zan so in ce, duniyarmu na da girman da ya ishi kasa da kasa, ciki har da Sin da Amurka su samu ci gaba tare, ba sai an ci nasara daga faduwar wani bangare ba. Kuma ya kamata a bari kasa da kasa su zabi hanyar ci gaba da suka ga ta dace.(Mai Zane:Mustapha Bulama)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki (2)

Next Post

Dubban Magoya Bayan Juyin Mulkin Nijar Sun Hallara A Filin Wasa Na Yamai

Related

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
Daga Birnin Sin

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

9 hours ago
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
Daga Birnin Sin

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

11 hours ago
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

12 hours ago
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

14 hours ago
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya
Daga Birnin Sin

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

15 hours ago
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 

17 hours ago
Next Post
Dubban Magoya Bayan Juyin Mulkin Nijar Sun Hallara A Filin Wasa Na Yamai

Dubban Magoya Bayan Juyin Mulkin Nijar Sun Hallara A Filin Wasa Na Yamai

LABARAI MASU NASABA

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

May 14, 2025
Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 14, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.