Karin magana na harshen Hausa su kan kunshi ma’ana mai zurfi. Misali “Kome nisan jifa, kasa zai fado.” Ana amfani da wannan karin magana wajen kwatanta yanayin farawar wani batu, da faduwarsa, gami da yadda ya kai karshe a wani yanayi da ba wanda zai iya magancewa. Kan haka ne nake dora alkalamina game da labarin da na ji na rufe hukumar taimaka wa aikin raya kasashe ta Amurka (USAID) a kwanakin baya, wanda nan take ya tuna min da wannan karin magana.
A cewar gwamnatin Amurka, hukumar USAID ta gaza tabbatar da cewa ayyukan da ta ba da kudin tallafi sun dace da muradun Amurka, bayan da ta shafe shekaru 64 tana aiki. Ban da haka, sakataren harkokin waje na kasar Amurka, Marco Rubio, ya ce hukumar ba ta cimma wani abu ba face kafa dimbin kungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGO) a duk fadin duniya. Kana a wuraren da ta shiga, ba a cika cimma burin raya kasa ba, yayin da yanayin rashin kwanciyar hankali kan ta’azzara, kuma kyamar Amurka na kara yaduwa.
- Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
- Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 50 A Benue
Sai dai kafin USAID ta fado kasa tamkar wani dutsen da kasar Amurka ta jefa, ta taba samun damar “tashi sama”, ma’ana cikin dogon lokaci hukumar ta zama daya daga cikin muhimman hukumomin da Amurka ke amfani da su wajen yin tasiri kan sauran kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, inda hukumar ta samar da kudi da karfafa kungiyoyin NGO, da kafofin watsa labaru, da cibiyoyin bincike, da dai sauransu. Kana a cikin ayyukan da USAID ta yi, har da tallafa wa cibiyar bincike dake adawa da kasar Sin ta kasar Austiraliya (ASPI), domin ta kirkira da yada jita-jita game da Sin, da ba da tallafi ga kungiyoyin NGO da ‘yan adawa na kasashen Ukraine da Georgia don kitsa sauyin mulki a kasashen. Sa’an nan, a watan Fabrairun bana, wani dan majalisar dokokin Amurka ya ce hukumar USAID ta taba samar da kudi ga kungiyoyin ‘yan ta’adda irin su Al-Qaeda, da Boko Haram ta Najeriya.
Amma a hakika, ban da wadannan miyagun abubuwa da muka ambata, USAID ita ma ta ba da wasu gudummawa, musamman ta fuskar kiwon lafiya. Misali, wani rahoton bincike da mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya “The Lancet” ta wallafa, ya yi hasashen cewa, raguwar kudin tallafin da aka samu sakamakon rufewar USAID, na iya haddasa mutuwar mutane fiye da miliyan 14 a duniya, ciki har da yara miliyan 4.5. Amma abin takaici shi ne, a ganin gwamnatin kasar Amurka ta yau, taimaka wa dorewar rayuwar mutane a kasashe masu tasowa “ba ta dace da muradun kasar Amurka ba”.
Hakika, da ma an san cewa tabbas Amurka za ta yi watsi da USAID. Saboda kasar ta kaddamar da shirin da zai samar da cikakken tasirinta a duniya a lokacin yakin cacar baka. Amma zuwa yanzu, tauraron kasar ya riga ya fara dishewa. Don haka ta yaya za ta samu isashen karfin cimma wani tsohon burinta da ta dade da sanyawa a rai? Idan an duba kudirin dokar “Babba kuma Kyakkyawa” (big and beautiful bill) da Amurka ta zartar kwanan nan, za a ga yadda kasar ta yi shirin rage kudin tallafin aikin jinya da na abinci, da sauran kudin tabbatar da jin dadin jama’a a cikin gidanta. Ta haka mun san cewa, ba za ta ci gaba da dora muhimmanci kan aikin jin kai a kasashen ketare ba.
Ta la’akari da wannan yanayin da kasar Amurka ke ciki, ma iya cewa, ita kanta ta zama kamar wani dutse ne da ke fadowa, kuma tabbas wata rana zai taba kasa! (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp