Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ta tallafa wa mutane 12,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Adamawa a shekarar 2022 da kayayyakin abinci iri daban-daban.
Tallafin wanda al’ummar Mayo-Ine a karamar hukumar Fufore ta jihar suka amfana, an yi shi ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar jin kai ta tarayya da kungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan “Kara Zurfafa Gyare-gyare A Sin Dama Ce Ga Duniya” Da Kuma Musayar Jama’a Tsakanin Sin Da Masar Na Shekarar Hadin Gwiwa
- Dangote Da BUA Za Su Bayyana A Gaban Majalisa Kan Badakalar Haraji
Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross na kasa, Prince Oluyemisi Adebayo Adeaga, ya bayyana a lokacin mika kayayyakin a hukumance a garin Mayo-Ine cewa, kowane magidanci zai karbi buhun shinkafa mai nauyin kilo 25, buhun garri 15kg, buhun wake 12kg., da man girki da manja kowanne lita biyar, sannan kuma akwai tsabar kudi har Naira 91,500.
Tallafin ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, za a raba shi ne ga gidaje 3,500 a fadin jihohin da lamarin yafi kamari da suka hada da Adamawa, Anambra, Kebbi, Oyo da Rivers.