Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta umarci rundunar ta da ta dauki mataki da nufin mayar da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar.
ECOWAS, ta bayyana hakan ne a lokacin da ta gabatar da kudurinta dangane da juyin mulkin da aka yi a Nijar a wani taro na musamman da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
- Golan Real Madrid Courtois Zai Yi Jinyar Watanni Bayan Samun Rauni
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Soke “Doka Game Da Taiwan”
Baya ga kiran daukar mataki, ECOWAS ta kuma yi kira ga kungiyar tarayyar Afrika (AU), da kasashen da ta ke hulda da kuma cibiyoyin da abin ya shafa da su goyi bayan kudurin da kungiyar ta dauka.
ECOWAS ta bayyana rashin jin dadinta ganin yadda duk wani yunkurin tattaunawa da gwamnatin mulkin soji a Nijar ya ci tura.
Bugu da kari, ECOWAS ta yi kakkausar suka ga ci gaba da tsare shugaba Mohamed Bazoum da ‘yan uwansa.
“Hukumar ta yi la’akari da takardar da shugaban ECOWAS ya gabatar kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar, da kuma yadda ECOWAS ta shiga tsakani tun bayan babban taronta na karshe;
“kuma mun yin la’akari da rahotannin wakilan Nijar da sauran wurare daban-daban;
“Mun yi la’akari da rahoto da shawarwarin kwamitin hafsoshin tsaro na ECOWAS;
“Mun tattauna kan sabon ci gaban da aka samu a Nijar tun bayan babban taron koli na karshe da aka gudanar a ranar 30 ga Yuli, 2023.
“An yi la’akari da cewa, duk kokarin diflomasiyya da ECOWAS ta yi, wajen magance rikicin, shugabannin sojin Jamhuriyar Nijar sun yi watsi da su.
“Sakamakon cikar wa’adin mako guda da aka bayar na mayar da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar mun yake wannan shawara.
“ECOWAS ta nanata kakkausar suka ga juyin mulki da kuma ci gaba da tsare Shugaba Mohammed Bazoam da iyalansa da kuma mambobin gwamnatinsa ba bisa ka’ida ba.
“Kaddamar da kudurin hukumar ECOWAS na warware rikicin.
“Tabbatar da duk matakai musamman na rufe kan iyakoki da tsauraran dokar hana tafiye-tafiye a kan duk mutane ko kungiyoyin mutanen da ayyukansu ke kawo cikas ga duk kokarin da ake na zaman lafiya da nufin tabbatar da ingantaccen tsarin mayar da tsarin mulki.
“Mun gargadi kasashe ta hanyar kawo cikas wajen warware rikicin Nijar cikin lumana game da illar matakin da suka dauka a gaban al’umma.
“Kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta amince da duk shawarar da hukumar ECOWAS ta dauka kan halin da ake ciki a Nijar.
“Dukkanin kasashe da cibiyoyin hadin gwiwa ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da su tallafa wa kungiyar ECOWAS, a kokarinta na tabbatar da mayar da tsarin mulkin kasar cikin gaggawa.”
ECOWAS ta jadadda aniyarta na tabbatar da mulkin dimokuradyya a Jamhuriyar Nijar.